Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da wata ziyarar aiki ta kwana biyu a kasar Masar daga 1 zuwa 2 ga watan satumbar da muke ciki, wannan ziyara kuma ita ce ta farko da Xi ya kai kasar Masar a tsawon shekaru 10, inda hakan ya yi dai-dai da cika shekaru 70 da kulla alakar difomasiyya tsakanin kasar Sin da Masar, wanda ya haifar da gagarumin cigaba bisa nasarorin da aka samu a baya, tare da mayar da hankali kan makomar kasashen biyu.
Yayin ziyarar, shugaban kasar Sin ya tattauna da da takwaran sa na Masar Abdel Fattah al-Sisi, inda suka cimma matsaya gami da shaida yadda aka sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa a fannoni da dama da suka hada da kirkirarriyar fasaha ta AI ,da hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki, da kuma hanyoyin safarar kayayyaki.
Kazalika shugabannin biyu sun kuma fitar da sanarwa ta cigaba da zurfafa alaka domin samar da cikakkun tsare tsaren hadin gwiwa.Bugu da kari shugabannin kasashen biyu sun yi tattaunawa mai zurfi game da yanayin da ake ciki a gabas ta tsakiya, inda shugaban kasar Sin ya gabatar da wasu manufofi guda hudu, domin gina sabon tsarin tsaro a gabas ta tsakiya.
Shugaba Xi ya jaddada samar da hadakar tsaron yanki ta bai daya, da kuma karfafa cikakkiyar hanyar jagorancin tsaron yanki, da bunkasa ginshikin ci gaban tsaron yanki, tare da habaka hadin kan kasa da kasa game da sha’anin tsaron yankin. Ta wannan hanya, kasar Sin ta nuna niyyarta ta cigaba da bayar da gudunmawa domin samar da mafita game da rikice-rikicen siyasa da ya dabaibaye gabas ta tsakiya.
A nan gaba kasashen Sin da Masar za su ci gaba da gina alaka tsakanin al’ummunsu mai tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya, da kuma kokarin samar da kyakkyawan tasiri a duniya. (Suleiman Suleiman Ibrahim)














