Dakarun Sojojin Nijeriya sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su, tare da kama wasu mutane shida da ake zargin ’yan ta’addan ISWAP ne da masu haɗin gwiwa da su a wasu samame daban-daban a jihohin Borno da Adamawa.
Wani rahoton ayyukan sojojin da aka bai wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a ranar Litinin ya ce an gudanar da samamen ne tsakanin 11 zuwa 13 ga Satumba, 2026.
Rahoton ya ce ayyukan sun kuma kai ga kama waɗanda ake zargin masu samar wa ’yan ta’addan kayan aiki da sauran masu taimaka musu, tare da lalata wasu bama-bamai (IEDs) da kuma kama wasu masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
ADVERTISEMENT













