Dakarun Haɗin Gwiwa na Operation Haɗin Kai sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP 103, tare da lalata manyan sansanoni da ma’ajiyar kayan aikinsu a wani gagarumin hare-hare ta sama na kwanaki takwas a yankin Arewa maso Gabas.
Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a birnin Maiduguri, inda ya tabbatar da cewa an ƙaddamar da hare-haren ne tsakanin ranakun 10 zuwa 18 ga watan Oktoba, 2026.
Bayanai sun nuna cewa an kai jerin hare-haren sama sau bakwai a maɓoyar ƴan ta’addar da ke Gudumbali a Ƙaramar Hukumar Guzamala, da Badu, da Mairari da Arina Woje a Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno, gami da Dutse Uku a Ƙaramar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa. Rundunar ta yi amfani da haɗin gwiwar jiragen yaƙi da na leƙen asiri marasa matuƙa (drones) wajen bibiyar motsin mayakan kafin luguden wutar.
Babban ci gaba da aka samu shi ne harin da aka kai a ranar Lahadi kan wurin ɓuyar Abu Saleem, babban kwamandan ISWAP na Kudancin Tafkin Chadi. Bayanan sirri sun tabbatar da mutuwar Jindullah, babban dogarin Abu Saleem, da Abul Kissa, mamba a Majalisar Ƙoli ta ƙungiyar (Shura Council), tare da ƙona injunan jiragen ruwa tara da tarin babura da ƴan ta’addar ke amfani da su.
Kaftin Goni ya jaddada cewa wannan sumame ya karya lagon ƙungiyar tare da tarwatsa tsarin shugabancinsu da dabarun sadarwa a yankin. Ya tabbatar da cewa dakarun sojojin Nijeriya za su ci gaba da matsa lamba ta sama da ƙasa domin murƙushe ragowar ƴan ta’addar da kuma tabbatar da dawo da cikakken zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.














