ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, October 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 8, Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Jihohi Uku

by Sadiq
57 minutes ago

Sojojin Operation FANSAN YAMMA sun kashe wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne guda takwas, tare da ceto mutane uku da aka sace a jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara.

Sojojin sun kuma ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, bindigogi uku ƙirar gida, babura uku, adduna da wasu layu.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Tamuno Sinivie ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

ADVERTISEMENT

A Jihar Katsina, sojoji sun kashe mutane biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne yayin musayar wuta a Ƙaramar Hukumar Sabuwa a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba.

Sun kuma ceto wani mutum mai suna Suleiman Umar, mai shekaru 42, wanda aka sace, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da babur guda ɗaya.

LABARAI MASU NASABA

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina

A Jihar Kaduna, sojoji da ke aiki tare da ’yan sa-kai na Civilian Joint Task Force sun kashe wasu mutane shida da ake zargin ’yan ta’adda ne bayan sun daƙile wani harin kwanton ɓauna a Ƙaramar Hukumar Igabi.

Rahotanni sun ce waɗanda ake zargin sun tsere da wasu mutane biyu a wani hari da suka kai a baya.

A Jihar Zamfara kuwa, sojoji sun ceto wasu mutane biyu, Shehu Chete, mai shekaru 40, da Bugu Bedi, mai shekaru 25, a garin Bagega da ke Ƙaramar Hukumar Anka, a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba.

An kai mutanen asibiti domin duba lafiyarsu kafin a miƙa su ga iyalansu.

Kyaftin Sinivie ya ce sojoji na ci gaba da sintiri da bincike domin kamo waɗanda suka tsere, ceto sauran mutanen da aka sace da kuma hana kai hare-hare.

Ya buƙaci mazauna yankunan da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai game da duk wani abu da suke zargi a yankunansu.

MASU ALAKA

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?
Tsaro

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

October 27, 2026
’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina

October 27, 2026
Dalilin da Ya Sa Harry Kane Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or
Wasanni

Dalilin da Ya Sa Harry Kane Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 27, 2026
Next Post
Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

LABARAI MASU NASABA

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

October 27, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 8, Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Jihohi Uku

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 8, Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Jihohi Uku

October 27, 2026
Amnesty International Da Ƙungiyar Matasan Arewa Sun Nemi A Yi Wa Sheikh Masussuka Adalci

Amnesty International Da Ƙungiyar Matasan Arewa Sun Nemi A Yi Wa Sheikh Masussuka Adalci

October 27, 2026
Gwamnan Katsina Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Sheikh Masussuka, Ya Nemi A Gudanar Da Bincike

Gwamnan Katsina Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Sheikh Masussuka, Ya Nemi A Gudanar Da Bincike

October 27, 2026
Ballon d’Or: Yamal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Matashin Ɗan Wasa Karo Karo Na Uku A Jere

Ballon d’Or: Yamal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Matashin Ɗan Wasa Karo Karo Na Uku A Jere

October 27, 2026
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu

Kotu Ta Tsare Wani Mutum Kan Zargin Barazanar Yaɗa Hotunan Tsiraicin Gwamnan Kano

October 27, 2026
’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina

’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina

October 27, 2026
Dalilin da Ya Sa Harry Kane Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or

Dalilin da Ya Sa Harry Kane Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 27, 2026
Sojoji Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

Sojoji Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

October 26, 2026
Kasar Sin Na Maraba Da Karin Kasashe Su Shiga Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya

Kasar Sin Na Maraba Da Karin Kasashe Su Shiga Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya

October 26, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.