Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi Allah-wadai da kisan malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, tare da kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
An ruwaito cewa wasu ’yan bindiga ne da ba a san ko su wane ne ba a kan babur, suka harbe malamin da wani abokinsa a ƙofar gidansa da ke Dutsin-Ma a daren ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, 2026.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Ibrahim Mohammed, ya fitar, gwamnan ya bayyana alhininsa kan kisan, tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Musulmi.
Radda ya buƙaci jami’an tsaro su gano tare da kama waɗanda suka aikata kisan.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen bincike.
Gwamnan ya bayyana marigayi Sheikh Masussuka a matsayin malamin addini mai daraja, wanda ya kasance yana koyar da zaman lafiya, fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kuma yin Allah-wadai da tsattsauran ra’ayi da tashin hankali.
Ya roƙi Allah Ya gafarta wa mamatan, Ya sanya su a Aljanna sannan Ya bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.














