Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International da Ƙungiyar Matasan Arewa ta Nijeriya sun yi kira da a yi adalci kan kisan malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a garin Dutsin-Ma na Jihar Katsina.
An ruwaito cewa wasu ’yan bindiga a kan babur ɗauke da makamai ne suka kashe malamin a ranar Litinin, lokacin da yake fitowa daga gidansa domin yin wa’azin kamar yadda ya saba yi da yamma.
Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan, tare da kira ga hukumomi da su gudanar da bincike cikin gaggawa da gaskiya, sannan su hukunta waɗanda aka samu da hannu a kisan.
Ƙungiyar ta ce Sheikh Masussuka ya kasance yana koyar da zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin Musulmi, tare da yin kira da a guji tsattsauran ra’ayi da tashin hankali.
Ta ƙara da cewa malamin ya sha fuskantar barazana da tsoratarwa a rayuwarsa.
Haka kuma, Ƙungiyar Matasan Arewa ta bayyana kisan a matsayin mummunan aiki, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Katsina da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ƙungiyar ta kuma nemi a kama tare da gurfanar da ’yan bindigar da suka kai harin da duk waɗanda ake zargin sun shirya ko suka ɗauki nauyin aikata laifin.
Shugaban ƙungiyar, Isah Abubakar, ya ce matasan Arewa za su sanya ido sosai kan binciken domin tabbatar da an yi wa malamin adalci.














