Dawowa daga hannun masu garkuwa da mutane na kawo sauƙi ga iyalai, amma ga waɗanda suka tsira, gwagwarmayar murmurewa na iya ci gaba. Raunin zuciya, matsalolin lafiya, tsadar rayuwa da kyama daga al’umma na daga cikin ƙalubalen da suke fuskanta.
A Nijeriya, musamman a yankin Arewa, labaran ceto mutanen da aka yi garkuwa da su kan jawo farin ciki da sauƙin zuciya ga iyalansu. Bayan kwanaki ko watanni na damuwa, iyalai kan sake rungumar ’yan’uwansu, yayin da al’umma ke murnar dawowarsu gida.
Sai dai, bayan an yi bikin dawowa, an ɗauki hotuna, an kuma yada labarin ceton, wata muhimmiyar tambaya kan taso: mene ne ke faruwa da waɗannan mutane bayan sun koma gida?
Bincike ya nuna cewa sakin mutum daga hannun masu garkuwa da mutane ba ya nufin cewa ya murmure gaba ɗaya daga abin da ya faru da shi. Wasu na komawa gida da raunukan jiki, matsalar barci, fargaba da tunanin abubuwan da suka faru a lokacin da suke tsare. Wasu kuma na fuskantar matsalolin kuɗi da wahalar sake saba wa rayuwar da suka bari.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar Àgídìgbo: ABUAD Journal of the Humanities a watan Yunin 2026, wanda ya mayar da hankali kan mutanen da suka tsira daga garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu ta Jihar Kebbi, ya nuna cewa iyalai, al’umma da addini na taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa waɗanda aka sako. Sai dai binciken ya kuma bayyana cewa matsalolin tunani da na tattalin arziki na iya ci gaba bayan dawowa gida, yayin da tallafin hukuma da na ƙungiyoyin agaji ke kasancewa a matsayin babban gibi.
Raunin da ba a iya gani
Ba duk raunukan da waɗanda aka sace suka samu ne ake iya gani a jikinsu ba. Wasu na iya dawowa ba tare da wata babbar alamar rauni ta zahiri ba, amma suna fama da tsananin fargaba da damuwa a zuciya.
Mutumin da ya fuskanci barazanar kisa, duka, yunwa ko rashin sanin lokacin da zai samu ’yancinsa na iya ci gaba da jin tsoro ko da ya koma gida. Wasu na fama da mafarkai masu tayar da hankali, rashin barci, saurin firgita da tsoron fita daga gida ko zama su kaɗai.
Wani rahoton Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) na shekarar 2024 ya bayyana yadda wani mutum da aka sace a Nijeriya, wanda ya shafe kwanaki 29 a hannun masu garkuwa da mutane, ya fuskanci mafarkai, rashin barci, fargaba da wahalar sake amincewa da mutane bayan an sake shi.
Bayan samun taimakon ƙwararrun ma’aikatan tallafa wa lafiyar tunani, ciki har da shawarwari da dabarun rage damuwa, mutumin ya fara koyon yadda zai shawo kan fargabarsa da sake gina rayuwarsa.
Wannan misali ya nuna cewa ceto mutum na iya zama farkon wani sabon mataki na murmurewa, wanda ke buƙatar lokaci da kulawa.
Lafiyar jiki da tunani na buƙatar kulawa
Bayan dawowarsu, ya kamata a duba lafiyar waɗanda aka sace domin gano raunuka, cututtuka, rashin abinci mai gina jiki ko wasu matsalolin da suka samu a lokacin da suke tsare.
Haka kuma, bai kamata a yi watsi da lafiyar tunaninsu ba. Ba kowane mutum ne zai bayyana damuwarsa a fili ba, kuma wasu na iya jin kunyar neman taimako saboda tsoron abin da mutane za su ce.
A binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta wallafa a ranar 7 ga Maris, 2025, ta bayyana labarin wata mata da aka sace tun tana yarinya a Jihar Borno, wadda ta shafe shekaru a hannun masu garkuwa da mutane kafin ta fara samun kulawar lafiya da tallafin tunani bayan dawowarta.
Rahoton ya nuna cewa illolin garkuwa da mutane na iya shafar rayuwar mutum na dogon lokaci, musamman idan ya fuskanci cin zarafi ko matsalolin lafiya yayin da yake tsare.
Saboda haka, taimakon waɗanda aka sako bai kamata ya tsaya ga duba lafiyarsu sau ɗaya kawai ba. Ya kamata a samar da hanyoyin da za su ba su damar samun kulawa a duk lokacin da suke buƙata.
Iyali da al’umma: Taimako ko ƙarin matsala?
Iyali na daga cikin manyan ginshiƙan da ke taimaka wa wanda aka sace ya sake samun kwanciyar hankali. Saurarensa ba tare da tilasta masa ba da labarin abin da ya faru ba, nuna masa ƙauna da taimaka masa wajen komawa ayyukansa na yau da kullum na iya sauƙaƙa masa murmurewa.
Sai dai, ba kowane martani daga al’umma ne ke taimakawa ba. Wani lokaci, mutane kan yi tambayoyi masu tayar da hankali, su yada bayanan sirri ko hotunan waɗanda aka sako ba tare da izininsu ba. Wasu kuma na iya zargin wanda aka sace ko yi masa kallon daban saboda abin da ya faru da shi.
Rahoton ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International na ranar 9 ga Yuni, 2024, ya bayyana yadda wasu ’yan mata da suka tsira daga hannun Boko Haram a Arewa maso Gabas suka fuskanci kyama da rashin isasshen tallafi yayin ƙoƙarin sake shiga cikin al’umma.
A wani labari da UNICEF ta wallafa a ranar 29 ga Janairu, 2024, wata matashiya mai suna Inna, wanda ba ainihin sunanta ba, ta bayyana yadda ta fuskanci zagi da ƙyama bayan dawowarta daga halin da ta shiga sakamakon rikicin Boko Haram.
Irin waɗannan matsaloli na iya sa waɗanda suka tsira su ware kansu daga mutane, su rasa damar samun ilimi ko aiki, ko kuma su kasa sake gina rayuwarsu yadda ya kamata.
Ya kamata iyalai da al’umma su fahimci cewa mutum ba shi da laifi saboda an sace shi. Yana buƙatar kulawa da mutunta sirrinsa, ba zargi ko kyama ba.
Matsin tattalin arziki bayan sakin waɗanda aka sace
Wani ƙalubalen da ake iya mantawa da shi shi ne tasirin garkuwa da mutane ga kuɗin iyali.
A wasu lokuta, iyalai kan sayar da kadarori, karɓar bashi ko kashe kuɗin da suka tara na tsawon shekaru domin biyan kuɗin fansa. Ko da an dawo da wanda aka sace, matsalar kuɗin da aka kashe na iya ci gaba da damun iyalin.
Ga wanda aka sace shi ma, idan ya rasa aikinsa, sana’arsa ko damar karatu, komawa rayuwar yau da kullum na iya zama da wahala. Wasu na buƙatar taimakon kuɗi, kayan aiki ko damar samun sana’a domin su sake dogaro da kansu.
Binciken da aka gudanar a Danko-Wasagu ya jaddada cewa taimakon iyali da al’umma yana da muhimmanci, amma ba koyaushe yake wadatarwa wajen magance matsalolin da waɗanda aka sace ke fuskanta ba. Wannan na nuna bukatar tsare-tsaren tallafi da za su taimaka wajen farfaɗo da rayuwar waɗanda abin ya shafa.
Me ya kamata gwamnati da hukumomi su yi?
Masana da rahotannin jin ƙai sun nuna muhimmancin haɗa ceto da tsarin kula da waɗanda aka sako. Wannan na buƙatar haɗin gwiwar hukumomin tsaro, ma’aikatan lafiya, ma’aikatan jin ƙai, ƙwararrun masu ba da shawara da shugabannin al’umma.
Da farko, ya kamata a tantance lafiyar waɗanda aka sako, a ba su kulawar gaggawa idan sun samu rauni, sannan a tura waɗanda ke buƙata wajen ƙwararrun masu kula da lafiyar tunani.
Na biyu, ya kamata a samar da tallafi na dogon lokaci, musamman ga yara, mata da waɗanda suka fuskanci tsananin cin zarafi ko suka shafe lokaci mai tsawo a tsare.
Na uku, ya kamata a taimaka wa waɗanda abin ya shafa su koma makaranta, su sake samun aiki ko su farfaɗo da sana’o’insu. Haka kuma, iyalansu na iya buƙatar tallafi idan sun shiga matsanancin hali sakamakon kuɗin fansa ko sauran kuɗaɗen da suka kashe.
Bugu da ƙari, hukumomi da ƙungiyoyin agaji ya kamata su kiyaye sirrin waɗanda aka sako, su guji bayyana bayanansu ba tare da izini ba, kuma su tabbatar da cewa tallafin da ake ba su ya dace da buƙatunsu.
Ceto ba shi ne ƙarshen tafiya ba
A ƙarshe, nasarar aikin ceto bai kamata a auna ta da yawan mutanen da aka sako kawai ba. Ya kamata a duba ko sun samu kulawar lafiya, sun farfaɗo daga raunin tunani, sun koma cikin iyalansu da al’ummominsu cikin mutunci, kuma sun sami damar ci gaba da rayuwarsu.
Kowane mutum na murmurewa ta hanyarsa. Wasu na iya farfaɗowa cikin ɗan lokaci, yayin da wasu ke buƙatar watanni ko shekaru kafin su sake samun cikakkiyar kwanciyar hankali. Saboda haka, bai kamata a matsa wa waɗanda aka sace su yi kamar komai bai faru ba.
Gwamnati, iyalai, ƙungiyoyin agaji da al’umma na da rawar takawa wajen tabbatar da cewa waɗanda suka tsira ba su tsaya a matsayin mutanen da aka ceto kawai ba, har ma sun sami damar sake gina rayuwarsu.
Domin a ƙarshe, sakin mutum daga hannun masu garkuwa da mutane mataki ne na farko. Taimaka masa ya warke, ya sake samun kwanciyar hankali da kuma rayuwa cikin mutunci shi ne ainihin cikar aikin ceto.














