Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Sanusi Dankaka a gidan gyaran hali na Kuje, bisa zargin yi wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, barazanar yaɗa bidiyo da hotunan tsiraicinsa a shafin Facebook.
Mai shari’a Salim Ibrahim ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin, bayan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da Dankaka a gaban kotun kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi laifuka a yanar gizo.
Sai dai Dankaka ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa DSS ta shigar da ƙarar ne a ranar 22 ga watan Oktoba, 2026, mai lamba FHC/ABJ/CR/699/2026.
Lauyan hukumar, Yusuf Afegbua ne, ya gabatar da ƙarar.
A cewar masu gabatar da ƙara, an aikata laifukan ne a watan Oktoban shekarar 2026, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.
A tuhuma ta farko, an zargi Dankaka da wasu mutanen da har yanzu ba a gano su ba da ƙoƙarin yaɗa abubuwan da ake ganin suna da illa ta wani shafi na Facebook mai suna Sanusi Dankaka Yahaya.
DSS ta yi zargin cewa Dankaka ya bayyana cewa yana da bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da yin barazanar sakin su.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa bayanan da ake yaɗawa ƙarya ne, kuma an yi hakan ne da nufin ɓata wa gwamnan suna, cin mutuncinsa da kuma cutar da shi.
DSS ta ce laifukan sun saɓa wa Dokar Laifukan Yanar Gizo ta shekarar 2015, wadda aka yi wa gyara.
Lokacin da aka fara shari’ar a ranar Litinin, lauyan DSS, Yusuf Afegbua, ya shaida wa kotun cewa a shirye suke su ci gaba da shari’ar.
Lauyan wanda ake ƙara, Kauna Penzin, ita ma ta tabbatar da cewa a shirye take domin yin shari’ar.
Bayan an karanta tuhume-tuhumen a gaban Dankaka, ya musanta aikata laifukan.
Daga nan, lauyan DSS ya nemi kotun ta tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.
Lauyan wanda ake ƙara bai yi adawa da wannan buƙata ba.
Mai shari’a Ibrahim ya amince da buƙatar, sannan ya ɗage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Disamba, 2026, domin fara sauraron shari’ar.
Saboda haka, Dankaka zai ci gaba da zama a tsare har zuwa lokacin da kotun za ta sake sauraron ƙarar.














