- Gabatarwa
Ilimin rubutu, wato amfani da zayyana wasu alamomi a kan takarda, ko a kan wani abu mai bagire don sadar da magana wadda ɗan’Adam ya fi faɗin ta da fatar baki, a ji shi da kunne, ya samu ne ga ɗan’Adam a wani lokaci mai tsawo, kuma ana amfani da alamomin rubutu iri-iri ne a sassa daban-daban na duniya, (Yahaya, 1988:1). A tarihi an fara rubuta Hausa cikin ajami ne, tun kafin Turawan mulkin mallaka su zo ƙasar Hausa. Shi ya sa ko da Turawa suka zo, wasunsu sai da suka yi amfani da rubutun ajami kafin dasa tsarin rubutun boko a ƙasar Hausa. An daɗe ana rubutun Hausa cikin boko ta bin hanyoyi mabambanta musamman ta fuskar haɗawa da raba kalmomi da sarrafa wasu sautukan da babu su a harshen Ingilishin da aka ari baƙaƙensa wajen ɗora lafazin Hausar. Wannan ya haifar da yunƙuri ta fuskoki daban-daban domin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa, ciki kuwa har da tarurruka a lokuta mabambanta. Wannan nazari ya bi zaren tarihi ne ta waiwayi waɗannan tarurruka tare da jaddada muhimmancin cigaba da gudanar da ire-irensu domin tabbatar da daidaito a rubutun Hausa musamman a wannan ƙarni na 21 da ilimin karatu da rubutu ya yawaita cikin al’umma, sa’annan kuma rubutun Hausa ke fuskantar barazana ta kauce wa ƙa’idojin rubutun, walau da gangan ko cikin rashin sani.
- Hausa Cikin Rubutun Boko: Ina Aka Fito?
A ƙasar Hausa an fara rubutu da ajamin Hausa tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Hanya ta biyu da aka ɗora lafazin Hausa a kai ita ce ta yin amfani da baƙaƙen Latin wanda ake kira boko. Rubutun boko tsarin rubutun abacada ne wato baƙaƙe da wasula a jere wanda ya samo asali daga Latin, wato harshen Romawa kimanin shekaru 3,131 da suka wuce. Asalin rubutun boko na Romawa ne kuma yanzu da shi Turawan Italiya da Faransa da Fotugal da Ingila da sauransu suke amfani, (Yahaya, 1988).
A ƙasar Denmark ta Turai ce aka fara rubuta kalmomin Hausa cikin rubutun boko, inda wani Baturen Denmark mai suna B.G Neighbuhr ya riƙa rubuta kalmomin Hausa yayin da yake koyon Hausa. Misali yakan rubuta kalmomi kamar haka:
- dudsji maimakon dutse
- ghurassa maimakon gurasa
- berni maimakon birni
- daua maimakon dawa, da sauransu. (Yahaya, 1988).
Turawan Mishan ne suka fara ƙarfafa boko da rubuta littattafai. Domin kuwa tarihi ya nuna cewa Turawan bincike da na Mishan sun rubuta harsunan Afirka da dama ta yin amfani da baƙaƙen Latin ciki har da Hausa. Waɗannan Turawa sun fara ziyartar Afirka ta yamma a cikin Ƙ18 ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna Ƙungiyar Gano Afirka.
Har ila yau, a cikin Ƙungiyar Gano Afirka da wasu ƙungiyoyin addinin Kirista na ƙasashen Turai sun cigaba da aiko Turawa daban-daban tun daga Ƙ18 zuwa Ƙ19 domin binciken al’adu da harsuna da kuma yaɗa addinin Kirista a Afirka ta yamma. Daga cikin irin waɗannan Turawa da suka yi rubuce-rubuce cikin harshen Hausa farkon Ƙ19 babu kamar Henrich Barth da James Frederick Schon. Daga cikin littattafan da Barth ya rubuta akwai;
- Collection of Vocabularies of Central African Languages (1862)
- Travels and Discoveries in North and Central Africa (3Vols), (195759), da sauransu.
Shi kuwa J.F Schon ya zo Afirka ne ƙarƙashin ƙungiyar yaɗa addinin Kirista mai suna ‘Church Missionary Society’ kuma ya rubuta littattafai kan harshen Hausa da wasu harsunan Afirka, kaɗan daga cikinsu akwai;
- Vocabulary of the Hausa Language (1843)
- Dictionaries of the Hausa Language (1876)
- Grammer of the Hausa Language (1862)
- Hausa Reading Book (1877)
- Magana Hausa (1885), da sauransu.
A shekarar 1891, Turawa sun kafa wata Ƙungiyar Hausa domin tunawa da wani jami’in yaɗa addinin Kirista mai suna Rev. John Alfred Robinson. Wannan ƙungiyar ce ta aiko Charles Henry Robinson ƙasar Hausa domin nazarin Hausa da adabin Hausa, shi kuma ya rubuta Nahawun Hausa da ƙamusu mai ɗauke da sassa na Ingilishi zuwa Hausa da kuma Hausa zuwa Ingilishi.
Akwai wasu Turawan da suka yi rubuce-rubuce cikin Hausar boko kafin Ƙ20 waɗanda suka haɗa da William Baikie wanda ya rubuta Letafi Zabura (1881) da J. Lippert ya rubuta Hausa (1886) da kuma J. Numa Rat ya rubuta The Elements of the Hausa Language (1889), (Yahaya, 1988; Bakura, 2018; Bunza, 2018).
Wannan ya sake jaddada cewa tun kafin Turawan mulkin mallaka, Turawa masu bincike da masu yaɗa addinin Kirista daga ƙasashen Ingila da Faransa da Jamus da Denmark sun yi amfani da baƙaƙen Latin sun yi rubuce-rubuce cikin Hausa. A lokacin da suke waɗannan rubuce-rubuce, Hausawa ba su fara rubuta Hausa cikin boko ba kuma Hausawa ba su san ma akwai wani irin rubutu na boko ba, sai da Turawan mulkin mallaka suka kafa makarantun boko a ƙasar Hausa.
- Tarurrukan Daidaita Ƙa’idojin Rubutun Hausa Daga Bamako Zuwa Yamai: Ina Ake?
Batun daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa ya samo asali tun a shekarar 1912. A wannan shekarar ne, Hanns Vischer (Ɗan Hausa) ya rubuta wani littafi mai suna Rules for Hausa Spelling inda ya zayyana ƙa’idojin rubutun Hausa a cikinsa, ya kuma bayyana irin kalmomin da suka kamata a raba da waɗanda suka kamata a haɗa. Sa’annan ya sauya ƙa’idojin rubuta waɗannan sautuka kamar haka:
- Maimakon b, a rubuta ‘b, wato ɓ
- Maimakon d, a rubuta ‘d, wato ɗ
- Maimakon k, a rubuta ‘k, wato ƙ
Waɗannan ƙa’idojin, su Mr. G.P Bargery ya bi wajen rubuta ƙamusunsa mai suna ‘Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary.’ Har ila yau kwamitin daidaita Ƙa’idojin Rubutun Hausa na shekarar 1932, ƙarƙashin jagorancin Farfesa D. Westermann ya shafe kusan shekara 5 kafin cim ma yarjejeniyar yi wa b da d da k ƙugiya suka koma ɓ da ɗ da ƙ, maimakon ɗige-ɗigen da HannsƁischer ɗin ya kawo a cikin littafin nasa, (Yahaya, 1988:126; Malumfashi da Mujaheed, 2018). An fitar da rahoton kwamitin mai suna Hausa Orthography wanda aka buga a mujallar gwamnati a shekarar 1938 (Ɓatagarawa, 2019).
Bayan wannan yunƙuri kuma sai kafa Hukumar Hausa a shekarar 1955 wadda jigonta shi ne daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa.Hukumar ta yi ayyuka da dama waɗanda suka haɗa da:
- Tabbatar da littafin ‘Rules for Hausa Spelling’ na Hanns Vischer (Ɗan Hausa).
- Cim ma yarjejeniya na daidaita wasu nahawun Hausa.
- Tsara littafi da ya ƙunshi yadda ake rubuta ararrun kalmomi.
- Fito da keɓaɓɓun kalmomi(Glossary Of Technical Terms). (Yahaya, 1988).
Daga bisani kuma sai batun shirya tarurruka domin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa ta tusgo, inda hukumomi irin su Hukumar Ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) da Majalisar Haɗin Kan Afirka (O.A.U) suka shirya tarurruka a mabambantan wurare da lokuta har sau huɗu; a Bamako ta ƙasar Mali da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da Jami’ar Bayero ta Kano a Nijeriya da kuma Yamai ta Jamhuriyar Nijar, tun daga shekarar 1966 zuwa shekarar 1980, (Yahaya, 1988; Ɓatagarawa, 2019).
Yahaya (1988), ya bayyana cewa duk da an buga ƙa’idojin rubutun Hausa cikin littafin Hausa Spelling wanda hukumar NORLA ta buga a shekarar 1958, da kuma gyare-gyaren da Hukumar Hausa ta yi wa ƙa’idojin aka buga a mujallar gwamnati, mutane sun cigaba da rubuta kalmomin Hausa barkatai musamman batun rabawa da haɗa kalmomi da kuma rubuta kalmomi da baƙaƙe iri daban-daban. Wannan matsalar ce ta haifar da gudanar da tarurruka domin duba waɗannan ƙa’idoji da yi masu gyare-gyare ta yadda za su sami karɓuwa har su bi jikin mutane. An gudanar da tarurrukan ne kamar haka:
- Bamako na ƙasar Mali, daga 28 ga watan Fabrairu zuwa 5 ga watan Maris na shekarar 1966.
- Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ranar 21 ga watan Yuni na shekarar 1970.
- Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano, a watan Satumba na shekarar 1972.
- Cibiyar Nazarin Harshe da Tarihi ta Sarrafa Adabin Baka[5] ƙarƙashin inuwar Majalisar Haɗa Kan Afirka (O.A.U), daga ranar 7 zuwa 12 ga watan Janairu na shekarar 1980. (Yahaya, 1988; Ɓatagarawa, 2019).
Waɗannan tarurruka sun yi alfanu sosai wajen fasalta karɓaɓɓen tsarin da ya samar da ƙa’idojin rubutun Hausa. Domin a ƙarshen tarurrukan, an tsara tare da tace duk ƙa’idojin rubutun Hausa, aka rattaɓa su dalla-dalla cikin rahoton taron ƙarshe na birnin Yamai ta Jamhuriyar Nijar domin amfani da su (ƙa’idojin) wajen rubuce-rubuce cikin Hausa.
Ƙa’idojin da aka fitar sun ƙunshi karɓaɓɓun baƙaƙe da wasulla manya da ƙanana da kuma auren wasali da tagwayen baƙaƙe. Sai kuma yadda ake rubuta manya da ƙananan baƙaƙe a wuraren da suka dace, da baƙaƙen nasaba da dangantaka da sauransu, (Yahaya, 1988).
4.0 Tafiyar Shekaru 41Daga Yamai Zuwa Kaduna (1980-2021): Ina Aka Dosa?
Daga abin da ya gabata, an fahimci cewa an ɗauki dogon lokaci kafin a kai ga matsaya kan ƙa’idojin rubutun Hausa da aka yarda da su a shekarar 1980. Idan aka lura da irin ƙoƙarin da magabata suka yi, za a ga cewa tarurrukan da aka yi domin tattauna batun ƙa’idojin rubutun Hausa sun haifi ɗa mai ido. Musamman ta la’akari da yadda aka samar da daidaito tsakanin ƙasar Nijar da ƙasar Nijeriya a wuraren da suka sami bambance-bambance wajen rubutunsu.
Wannan ya nuna cewa batun ƙa’idojin rubutu al’amari ne da yake buƙatar hannu da yawa da kuma sake bita lokaci bayan lokaci domin tabbatar da daidaito. Alal misali, cikin shekaru 14 Daga 1966 zuwa 1980, an gudanar da tarurruka domin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa har sau 4, cikin ƙasashe uku na Hausawa da kuma ma’abota Hausar. Kuma an gudanar da tarurrukan ne tare da masu-ruwa-da-tsaki a harkar rubutun Hausa; tun daga masana da manazarta da marubuta da kuma gudummawar hukumomi na gida da na ƙasashen waje irin su O.A.U da UNESCO. Sai dai me? Tsawon shekaru 39, tun daga shekarar 1980 zuwa 2019, ba a sake gudanar da irin wannan taro ba, duk kuwa da ana samun ɓullar sababbin kalmomi da ɓullar sabubba da suke haifar da kauce wa ƙa’idojin rubutun Hausa. Ga kuma matsalar rashin daidaito wajen rubutu musamman a kafafen watsa labarai da kuma hawan ƙawara da wasu marubutan suke yi wa rubutun Hausa[6].
Wannan takarda tana da fahimtar cewa, ta hanyar shirya tarurrukan ƙara wa juna sani a kai- a kai, musamman a kan ƙa’idojin rubutun Hausa kacokam ne hanya mafi sauƙi da kuma muhimmanci wajen daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa da kuma jaddada shi da yayata shi, har masu tu’ammali da rubutun na Hausa su lura kuma su amshi ƙa’idojin har su bi jiki.
Saboda haka, Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe na Jami’ar Jihar Kaduna a taron da ya gudanar a shekarar 2019, ya yi susa a gurbin ƙaiƙayi. Domin kuwa duk da cewa taron ba domin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa ba ne kawai, a’a, taron ƙara wa juna sani ne kan ƙa’idojin rubutun Hausa da daidaitacciyar Hausa da kuma abin da ya shafi kalmomin Hausa. Duk da haka, taron ya samar da wata kafa ta tattauna batutuwan da suka shafi ƙa’idojin rubutun Hausa tare da samar da wata taska da za a iya laluba domin sake fasalta ƙa’idojin rubutun Hausa, don tabbatar da daidaito a rubutun Hausa a wannan ƙarni na 21.
Har ila yau, an sake gudanar da taro na musamman kan daidaitacciyar Hausa da sabunta ƙa’idojin rubutun Hausa wanda Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyar Harshe na Jami’ar Jihar Kaduna ya jagoranta a NTI Kaduna cikin shekarar 2021. An gudanar da taron ne domin samar da matsaya a ga batutuwan da aka tattauna a taron Kaduna na shekarar 2019, inda masana da malamai da ɗalibai waɗanda aka zaƙulo daga sassa daban-daban masu tu’ammali da ƙa’idojin rubutun Hausa, suka haɗu domin samun matsaya.
- Kammalawa
A wannan nazari an tattauna batun rubutun Hausa ne, musamman abin da ya shafi tarurrukan da aka gudanar domin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa cikin tarihi. An bayyana yadda aka fara rubutun Hausa cikin harrufan Latin(boko) da kuma yadda aka shimfiɗa wa rubutun Hausa ƙa’idoji bayan tarurrukan da aka gudanar har sau biyar tun daga shekarar 1966 zuwa 2021. A ƙarshe aka yi tsokaci kan muhimmancin cigaba da gudanar da irin waɗannan tarurruka domin sabuntawa da kuma daidaita sababbin ƙa’idojin rubutun Hausa, musamman a wuraren da akan sami bambance-bambance tsakanin masu tu’ammali da rubutun Hausa a fagen nazari da kafafen watsa labarai da hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da ma ɗaiɗaikun mutane. An jaddada cewa ire-iren waɗannan tarurruka, sun gudana daidai lokutan da ake buƙata domin sun zama tamkar matattakala da aka hau aka samar da tsanin da ya zama dabashirin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa. Domin an yi irin wannan yunƙuri a baya an ga alfanunsa. Ke nan waiwayen jiya, zai ba yau damar fasalta gobe da jibi.
Abdullahi Mujaheed, PhD
Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
Waya: +2348069299109
i-mel:[email protected]














