Tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya ce Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ba shi da ƙarfin da zai kawo ƙarshe siyasarsa.
Da yake zantawa da BBC Hausa, Goje ya ce Allah ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen makomar siyasarsa.
Ya ce ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba bayan ya rasa tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC, amma zai ci gaba da goyon bayan jam’iyyar.
Goje ya ce ya shafe shekaru masu yawa yana siyasa, kuma yana ganin lokaci ya yi da ya kamata a bai wa matasa damar fafatawa a siyasa.
Sai dai ya jaddada cewa har yanzu zai iya komawa Majalisar Dattawa idan ya yanke shawarar tsayawa takara kuma ya samu tikiti a kowace jam’iyya.
Tsohon gwamnan ya kuma musanta cewa an ci amanarsa, yana mai cewa ya amince da rasa tikitin takara a APC a matsayin ƙaddara daga Allah.














