ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

by Abba Ibrahim Wada
2 months ago
VAR

An fara amfani da na’urar VAR ne a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a shekarar

2018 kuma ta shiga tsakani sau 20 a wasanni 64 da aka buga tun farkon fara gasar har karshe. BAR ta sauya hukunce-hukuncen alkalan wasa sau 17, ciki har da muhimmin al’amura a wasan karshe: lokacin da Faransa da Croatia su ke kunnen doki

1-1 na’urar ta sa alkalin wasa ya sauya hukuncin da ya yanke daga taba kwallo da hannu a wajen da’ira ta 18 zuwa bayar da bugun fenariti.

ADVERTISEMENT

Faransa ta zura kwallon, inda ta shige gaba da ci 2-1 a wasan da daga karshe ta lashe wasan da ci 4-2. A gasar cin kofin dauniya da aka buga a Katar, shekaru hudu bayan haka, an yi amfani da VAR sau 27. Lokacin da aka bai wa alkalin wasan shawarar ya duba na’urar gefen fili, alkalin wasa ya suya hukuncinsa a dukkan lokuta ban da sau biyu kacal.

Na’urar da ke taimaka wa alkalin wasa na bidiyo (VAR) ta kasance babbar abin tattaunawa a gasar cin kofin duniya ta 2026, amma muhawara kan amfaninta ko akasin haka ya kai wani sabon mataki ne bayan nasarar da Argentina ta samu kan Masar a wasan zagaye na ‘yan 16 a ranar 7 ga watan Yuli.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Kasar ta Afirka, ta jagoranci wasan da ci 2-0 har zuwa lokacin da ya rage saura minti 11a tashi wasan kafin Argentina ta farfado ta ci kwallo uku a karshen wasan, lamarin da ya sa Masar ta fusata bayan an kashe kwallon da ta ci, da kuma ikirarin cewa an hana ta bugun fenariti a karshen wasa, wanda BAR ba ta shiga tsakani ba.

Kocin Masar, Hossam Hassan ya ce watakila suna son masu rike da kambun gasar su ci gaba da kasancewa a gasar. Watakila suna son Messi ya ci gaba da fafatawa a gasar.

‘Yan wasan Masar sun fusata musamman da hukuncin da aka yi musu na hana kwallon da Mostafa Zico ya ci a rabin lokaci na biyu lokacin da suke kan gaba da ci 1-0, bayan da aka hukunta dan wasan tsakiya Marwan Attia saboda taka Lisandro Martinez kafin a ci kwallon.

‘Yanwasan sun dage cewa an yi wa Mohamed Salah keta a irin wannan da’ira ta 18 din Argentina ‘yan dakika kadan kafin masu rike da kambun gasar su ci kwallonsu ta uku, amma ba a dauki wani mataki ba. A dukkan wadannan abubuwan da suka faru, an yi tambaya game da rawar da BAR ke takawa a gasar ta bana.

Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta fara amfani da na’urar (VAR) a hukumance a shekarar 2018, inda shugaban hukumar Gianni Infantino ya yaba da ita a matsayin wata sabuwar fasaha da za ta taimaka wa alkalan wasa yanke hukuncin da ya dace.

A takaice dai, yin amfani da fasahar bidiyo ne don tallafa wa alkalan wasa a filin wasa a lokacin wani abu ya faru da ba su iya gani a lokacin da ya faru ba, wanda kuma ya kai ga an yi kuskure a yanke hukunci da zai yi tasiri kan wasan. Fasahar ta bai wa alkalan wasa damar yin bitar bidiyo daga kyamarori da dama sannan su yanke hukunci kan ko sun yi kuskure a hukuncin da suka yanke.

Ana amfani da ita a cikin gasa sama da 300 a fadin duniya, a cewar FIFA.

Tawagar alkalan wasa na nazarin bidiyo a dakunan gudanar da ayyukan bidiyo da ke nesa da ainihin filayen wasa – a fagen gasar cin kofin duniya ta 2026, an ajiye su a wata cibiyar yada labarai a birnin Dallas.

Ana iya umurtar alkalan wasa don kallon bidiyon da suka dace akan talabijin na musamman da aka ajiye a gefen filin wasa. Alkalin wasa da ke cikin filin zai yanke hukunci na karshe bayan ya yi wannan bitar.

Kafin gasar 2026, ana iya amfani da na’urar VAR ne kawai a yanayi hudu: cin kwallaye, yanke hukunci kan bugun fenariti, abubuwan da suka faru na jan kati da kuma magance kuskure wurin gane ‘yanwasa.

Na biyar, wanda FIFA ta bayyana a matsayin “bayar da bugun kusurwa bisa kuskure”, an kara shi cikin jerin al’amuran, kuma yanzu ana amfani da VAR don duba idan an bayar da katin gargadi na biyu wanda zai zama jan kati.

BAR ba ta da wani tasiri wajen tantance ko kwallon ta ketare layi ko a’a. Wani tsarin yana duba wannan ta hanyar amfani da na’uran da aka sanya a cikin kwallon don sanar da alkalan wasa kai tsaye ta hanyar agogon da suke sanye da shi a hannunsu.

Yadda ake amfani da ita a gasar bana

Ganin cewa har yanzu gasar ta bana ba ta kare ba, babu cikakkun bayanai. Amma wani bincike da aka yi, ya gano cewa alkalan wasa sun je wurin na’urar sanya ido a filin wasa sau 23 a wasanni da aka buga zuwa yanzu a wannan gasar cin kofin duniya mai tsawo (jimilla wasanni 104).

Shiga tsakani daya ne kawai bai yi sanadiyar sauya hukuncin alkalin wasa na farko ba.

A makon da ya gabata ne Pierluigi Collina, shugaban alkalan wasa na FIFA, ya jaddada muhimman ka’idoji da aka bai wa jami’ansa. Ya ce an gaya wa alkalan wasa su bar cudanya tsakanin ‘yanwasa da bai wuce misali ba, don bari wasanni su gudana cikin sauri.

Gasar cin kofin duniya ta 2026 ta kuma ga karancin bugun tazara da aka bayar a kowane wasa (22.6) idan aka kwatanta da gasa biyu da suka gabata (25 a 2022 da 27 a 2018). Rashin amincewa da cin da Masar ta yi, BAR bai yi daidai ba da yadda ake yin alkalancin wasa a gasar ba zuwa yanzu.

VAR
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Sabon Tsarin Tikitin Abinci Na Nusuk Zai Iya Ƙara Kuɗin Bizar Umrah

Sabon Tsarin Tikitin Abinci Na Nusuk Zai Iya Ƙara Kuɗin Bizar Umrah

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.