Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain PSG, wadda ita ce za ta kara a kofin, tare da manyan kungiyoyi irin su Manchester City, Aston Billa da Barcelona a matakin league phase na Champions League na wannan kakar.
PSG za ta karbi bakuncin Barcelona a Parc des Princes, sannan kuma ta yi tafiye-tafiye zuwa Billa Park da Manchester domin fuskantar Aston Billa da Manchester City. Kungiyar Arsenal za ta fuskanci Real Madrid da Bayern Munich, Zakarun Premier League Arsenal za su karbi bakuncin Real Madrid a Emirates Stadium, sannan su yi tafiya zuwa Jamus domin karawa da Bayern Munich.
Kungiyar Mikel Arteta za ta kuma kara da Borussia Dortmund, Real Betis, Lille, Napoli, Sabah da Slabia Prague. Manchester City za ta sake haduwa da Rodri da De Bruyne, za ta karbi bakuncin PSG a Etihad Stadium sannan ta yi tafiya zuwa Barcelona, inda za ta kara da tsohon dan wasanta Rodri, wanda ya koma Barcelona a wannan bazarar.
Ita kuwa Manchester City kuma za ta fuskanci Napoli, inda za ta sake haduwa da tsohon tauraronta Kebin De Bruyne sai kuma sauran abokan karawarta da suka hada da Sporting CP, Porto, RB Leipzig, AEK Athens da Lens.
Kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa wadda ta lashe kofin Europa League ta dawo Champions League za ta karbi bakuncin PSG da Borussia Dortmund, sannan ta yi wasannin waje da Barcelona da Galatasaray. Sauran kungiyoyin da za ta kara da su su ne Club Brugge, Fenerbahce, Biking da Slabia Prague.
Manchester United ta dawo gasar bayan shekaru biyu za ta kara da Bayern Munich, Atletico Madrid, Roma, Sporting CP, RB Leipzig, Billarreal, Sabah, Como. Sai Liberpool za ta kara da Atletico Madrid da Inter Milan za ta karbi bakuncin, Atletico Madrid, Porto, Billarreal, Lens Sannan za ta yi wasannin waje da Inter Milan, Club Brugge, Fenerbahce, LASK.
Kamar yadda hukumar kwallon kafa ta Eufa ta tsara, za a fara wasannin rukunin matakin farko ne a ranar 8 ga Satumba, yayin da zagayen karshe zai gudana ranar 27 ga Janairu, 2027.
Wadanne Kungiyoyi Ne Za Su Fuskanci Na Premier?
Arsenal: Real Madrid (a gida) Bayern Munich (a waje) Borussia Dortmund (a gida) Real Betis (a waje) Lille (a gida) Napoli (a waje) Sabah (a gida) Slabia Prague (a waje). Aston Billa: PSG (a gida) Barcelona (a waje) Borussia Dortmund (a gida) Club Brugge (a waje) Fenerbahce (a gida) Galatasaray (a waje) Biking (a gida) Slabia Prague (a waje).
Liberpool: Atletico Madrid (a gida) Inter Milan (a waje) Porto (a gida) Club Brugge (a waje) Billarreal (a gida) Fenerbahce (a waje) Lens (a gida) LASK (a waje) Manchester City: PSG (a gida) Barcelona (a waje) Sporting CP (a gida) Porto (a waje) Napoli (a gida) RB Leipzig (a waje) AEK Athens (a gida) Lens (a waje) Manchester United: Bayern Munich (a gida) Atletico Madrid (a waje) Roma (a gida) Sporting CP (a waje) RB Leipzig (a gida) Billarreal (a waje) Sabah (a gida) Como (a waje).
A sabon tsarin Champions League, kowace kungiya daga cikin kungiyoyi 36 za ta buga wasanni takwas da kungiyoyi takwas daban-daban a matakin league phase, inda za ta buga wasanni hudu a gida da hudu a waje. Kungiyoyin da suka kammala a cikin manyan takwas na teburin gasar za su tsallaka kai tsaye zuwa zagayen ‘yan 16. Wadanda suka zo daga matsayi na tara zuwa na 24 kuwa za su buga wasannin neman gurbi gida da waje domin samun damar shiga zagayen ‘yan 16.
Kungiyoyin da suka kammala daga matsayi na 25 zuwa kasa za su fita daga gasar gaba daya, kuma ba za su sauka zuwa gasar Europa League ba. A kakar wasan da ta gabata, Arsenal wadda ta kai wasan karshe ita ce ta zo ta daya a teburin league phase da maki 24 bayan ta yi nasara a dukkan wasanninta takwas.
Liberpool ta zo matsayi na uku da maki 18, bayan Bayern Munich da ta zo ta biyu, yayin da Tottenham ta kammala a matsayi na hudu da maki 17. Chelsea da Manchester City su ma sun tsallaka kai tsaye zuwa zagayen ‘yan 16 bayan sun kammala a matsayi na shida da na takwas bi da bi, yayin da Newcastle ta zo ta 12.
Sai dai Chelsea, Manchester City, Newcastle da Tottenham duk sun fita daga gasar tun a zagayen ‘yan 16 a kakar da ta gabata. Liberpool kuwa PSG ta fitar da ita a wasan kwata-fainal.
Daga baya PSG ta kai wasan karshe inda ta sake doke kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ta kuma lashe kofin Champions League karo na biyu a jere, abin da kungiyar bata taba yi ba.














