Ambaliyar ruwa da ta afku a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutane huɗu, yayin da ake ci gaba da neman wasu huɗu da suka ɓace bayan ruwan sama mai tsanani da ya mamaye sassan birnin.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) ya ruwaito cewa ambaliyar ta janyo babbar barna a gidaje, shaguna, tituna da wuraren jama’a, tare da mamaye motoci da kuma kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.Rahoton ya bayyana cewa ruwan sama mai tsanani da aka samu cikin sa’o’i 48 ya zarce jimillar matsakaicin ruwan sama da aka saba samu a watannin Satumba da Oktoba a yankin.
Daga cikin waɗanda suka rasu akwai wani mutum mai shekaru 66 da aka gano gawarsa a ƙarƙashin wata gada, da kuma wani matashi da ya mutu sakamakon girgizar lantarki.Ruwan ya kuma mamaye ƙananan hanyoyi da wuraren da jama’a ke amfani da su, yayin da wasu motoci suka kwashe da ruwa suka taru a ƙasan titunan da ke gangara.
Rahoton ya ce hukumomi sun karɓi kusan rahotannin asarar dukiya 10,000, yayin da aka tura jami’an agajin gaggawa da sauran ma’aikata kusan 46,000 domin aikin ceto, taimakawa waɗanda abin ya shafa da kuma gyara barnar da aka samu.
Hukumomin Turkiyya sun kuma yi gargaɗin yiwuwar sake samun ruwan sama mai ƙarfi a Istanbul da wasu yankunan da ke makwabtaka da shi, lamarin da ya sa aka buƙaci mazauna yankunan da su ƙara taka-tsantsan.
Ministan Muhalli na Turkiyya, Murat Kurum, ya bayyana sauyin yanayi a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara tsananta matsalolin ruwan sama mai yawa, tare da jaddada buƙatar ɗaukar matakan da za su rage illolin ambaliyar ruwa.
Haka kuma, hukumomi sun ci gaba da ayyukan agaji da tantance barnar da ambaliyar ta haifar, yayin da ake sa ido kan yanayin ruwan sama a yankunan da abin ya shafa.














