Kamfanin TikTok ya musanta cewa shi ne ya hana mutane amfani da manhajarsa a wasu sassan Arewacin Nijeriya, yana mai cewa yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin magance matsalar.
Masu amfani da TikTok a jihohin Kaduna, Kano, Kebbi da Sokoto sun koka kan matsalar kasa shiga manhajar tun daga watan Satumba.
Wasu sun ce sai sun yi amfani da manhajar VPN kafin su samu damar yin amfani da shi.
TikTok ya ce ba shi ne ya sanya takunkumin ba, amma bai bayyana abin da ya jawo matsalar ko lokacin da ake sa ran za a dawo da amfani da manhajar yadda aka saba ba.
Masu amfani da manhajar sun ce bidiyoyi ba sa buɗewa, sannan suna fuskantar matsaloli wajen ɗora sabbin bidiyoyi.
Ƙungiyoyi sun yi kira da a fayyace musabbabin matsalar da ta hana wasu mutane amfani da TikTok yadda ya kamata.














