Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ta ƙasa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a shekarar 2027. Ya ce nazarin masana harkokin siyasa da yanayin siyasar ƙasar a halin yanzu na nuna hakan.
Barau ya bayyana wannan matsaya ne ranar Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026, yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado na Jihar Kano. Ya buƙaci mambobin jam’iyyar su haɗa kai wajen neman nasarar dukkan ’yan takararta a zaɓen 2027.
Sanatan ya yaba wa shugabannin APC, zaɓaɓɓun wakilai, da shugabannin ƙananan hukumomi da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar. Ya kuma ce sauya sheƙar Gwamna Abba daga NNPP zuwa APC mataki ne da ya ƙara wa Kano muhimmancin siyasa tare da buɗe mata ƙarin damar samun ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya.
Barau ya bayyana cewa Kano na daga cikin jihohin da suka fi yawan masu rijistar zaɓe a Nijeriya, don haka ta cancanci kulawa ta musamman daga gwamnatin tarayya. Ya ce haɗin kan gwamna, da ƴan majalisar tarayya da jiha, shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli ƙarƙashin APC na iya taimakawa wajen samar da ayyukan ci gaba ga al’ummar jihar.
Ya kuma bayyana cewa an haɗa shugabannin jam’iyya, da tsofaffi da sabbin ƴan majalisa, da kansiloli, da shugabannin ƙananan hukumomi da dattawa cikin kwamitocin yaƙin neman zaɓen. Ya buƙaci mambobinsu su fara tattara masu zaɓe da wayar da kan jama’a domin neman nasarar ƴan takarar APC daga matakin shugaban ƙasa har zuwa sauran mukamai.














