ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 2, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Fara Farautar Maharan Da Suka Kashe Abokin Aikinsu A Filato

by Abubakar Sulaiman
51 minutes ago
Sojoji

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙaddamar da farautar wasu mahara da suka kai hari kan shingen binciken ababen hawa na sojoji a Sopp, Ungwan Boka, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato, inda suka kashe soja ɗaya tare da kwashe makamai. Dakarun da ke ƙarƙashin rundunar Operation Enduring Peace ne ke gadin shingen a lokacin da aka kai harin.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026. Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun buɗe wa sojojin wuta daga wurare daban-daban, lamarin da ya haifar da musayar wuta kafin maharan su tsere zuwa dazukan da ke kewaye da yankin.

Kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya tabbatar da faruwar lamarin a Jos ranar Lahadi, inda ya bayyana harin a matsayin wanda aka shirya da gangan kuma ba tare da wani dalili ba. Ya ce sojojin sun dawo da zaman lafiya a yankin, kuma sun fara bin sawun maharan domin cafke su da kuma ƙwato makaman da suka kwashe.

ADVERTISEMENT

Oteh ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ƙara sanya ido a yankin domin hana sake samun irin wannan hari da kuma tabbatar da tsaron mazauna garin. Ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, tare da kai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano maharan.

A nasu ɓangaren, wasu mazauna yankin sun yi Allah-wadai da harin, inda suka buƙaci hukumomin tsaro su kamo waɗanda suka aikata shi. Sun bayyana damuwarsu kan kashe sojan, tare da cewa shingen binciken na taimakawa wajen daƙile ayyukan masu aikata laifuka a yankin.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

Sojoji
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mutane Tara Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Sama Kusa Da Gidan Hutu Na Trump A Florida
  • Abubakar Sulaiman
    Biyan Bashin Wutar Lantarki Da Muka Yi Ya Farfaɗo Da Amincewar Masu Zuba Jari – Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

MASU ALAKA

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC
Manyan Labarai

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

November 1, 2026
Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

November 1, 2026
kano
Manyan Labarai

Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano

November 1, 2026
Next Post
Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaki Ya Rasu A Hatsarin Mota Watanni Uku Bayan Zaɓansa

November 2, 2026
Sojoji Sun Fara Farautar Maharan Da Suka Kashe Abokin Aikinsu A Filato

Sojoji Sun Fara Farautar Maharan Da Suka Kashe Abokin Aikinsu A Filato

November 2, 2026
Mutane Tara Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Sama Kusa Da Gidan Hutu Na Trump A Florida

Mutane Tara Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Sama Kusa Da Gidan Hutu Na Trump A Florida

November 2, 2026
Biyan Bashin Wutar Lantarki Da Muka Yi Ya Farfaɗo Da Amincewar Masu Zuba Jari – Tinubu

Biyan Bashin Wutar Lantarki Da Muka Yi Ya Farfaɗo Da Amincewar Masu Zuba Jari – Tinubu

November 2, 2026
Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

November 1, 2026
Sin Ta Fitar Da Cikakken Tsarin Sauka A Duniyar Wata

Sin Ta Fitar Da Cikakken Tsarin Sauka A Duniyar Wata

November 1, 2026
Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

November 1, 2026
Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

November 1, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba

November 1, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Ranar Biranen Duniya

Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Ranar Biranen Duniya

November 2, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.