Shugaban ƙaramar jukumar Zaki da ke Jihar Bauchi, Mallam Masud Aliyu Umar, ya rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a lokacin da yake hanyar komawa gida Zaki daga Bauchi bayan halartar wani taron siyasa, watanni uku kacal bayan zaɓensa.
Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya afku ne a yammacin ranar Lahadi a ƙauyen Konkiyal da ke ƙaramar hukumar Darazo ta jihar.
Marigayin na kan hanyarsa ta komawa Zaki ne bayan halartar wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APM, wanda jam’iyyar ta kira a ranar Lahadi a Bauchi, lokacin da hatsarin ya rutsa da shi.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa an zaɓi Masud Aliyu Umar a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Zaki a ranar 17 ga watan Agusta, 2026, tare da sauran shugabannin ƙananan hukumomi 19 na jihar.
Kafin zaɓensa, ya taɓa riƙe mulamin darakta-janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA).
Da ya ke isar da saƙon ta’aziyyarsa, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana alhini da kaɗuwa matuƙa bisa wannan mummunan rashi.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harƙoƙin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, gwamnan, a madadin iyalansa, gwamnatin jihar da al’ummar Bauchi, ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar ƙaramar hukumar Zaki, Majalisar Masarautar Katagum, ALGON reshen Jihar Bauchi, da abokansa, makusantansa da abokan huldarsa na siyasa.
Gwamna Mohammed ya bayyana marigayi Umar a matsayin ɗan siyasa mai kishin ci gaban jama’arsa da ƙasa baki ɗaya.
Da yake tunawa da rawar da ya taka a baya a matsayin Darakta-Janar na SEMA, gwamnan ya ce marigayin ya nuna ƙwazo da jajircewa wajen ba da agajin gaggawa, kula da ibtila’o’i da kuma tallafa wa al’ummomin da suka fuskanci matsalolin jin ƙai a faɗin jihar.
Ya ce, “Lokacin da yake jagorantar SEMA, ya nuna sadaukarwa wajen rage radadin wahalhalun al’ummar da ke cikin mawuyacin hali, tare da samar da agajin gaggawa ga al’ummomin da ibtila’o’i da sauran matsalolin jin kai suka shafa.”
Gwamnan ya ƙara da cewa, a matsayinsa na shugaban ƙaramar hukumar Zaki, Umar ya ci gaba da nuna cikakken jajircewa wajen bunƙasa al’umma, musamman ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa matasa da mata, inganta hanyoyin samun abin dogaro da kuma tabbatar da ci gaba mai hada kowa da kowa.
Ya bayyana cewa duk da cewa wa’adinsa na shugabancin karamar hukumar bai daɗe ba, amma kishinsa na yi wa jama’a hidima, kusancinsa da al’umma da kuma jajircewarsa wajen inganta rayuwar al’ummar da yake wakilta sun bambanta shi da sauran shugabanni.
Gwamna Mohammed ya kuma bayyana cewa rasuwar marigayin ba babban rashi ba ne ga iyalansa da al’ummar ƙaramar Hukumar Zaki kadai, illa ma babban rashi ne ga Jihar Bauchi baki ɗaya, musamman bangaren ma’aikatan gwamnati da gudanar da kananan hukumomi.
Ya roki Allah cikin rahamarsa marar iyaka da Ya gafarta masa kurakuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, sannan Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026, da ƙarfe 2:00 na rana, a fadar Dagacin Mur Mur, da ke ƙaramar hukumar Zaki ta Jihar Bauchi.














