ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
Infantino

Ga wani sharhin da aka wallafa a jaridar Helsinkitimes na Finland a ran 13 ga watan Yuni.

Gasar cin kofin duniya ta hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, wadda Amurka, Kanada da Mexico suke karbar bakunci tare, tana gab da ƙarewa. A cikin shekaru ɗari na tarihin FIFA, wannan ita ce gasa mafi nasara, kuma mafi rikicin da aka taba gudanarwa. Ƙarin adadin ƙungiyoyin da suka shiga da kuma yawan wasanni sun kafa sabbin tarihi, haka ma yawan masu kallo da kudaden shiga na kasuwanci. A matsayinsa na shugaban FIFA na tara, Gianni Infantino yana da dalilai masu yawa na yin bitar abin da za a iya kira da jerin “nasarorin tarihi.”

Amma wani batu na gaskiya, wanda kuma ba za a iya musantawa ba ya fito fili: A tsakiyar rikicin da ke tattare da gasar, mutane sun fahimci cewa rikici na ƙara girma. Ko Infantino da abokan aikinsa za su yarda a bainar jama’a ko a’a, wataƙila wannan gasa ta zamewa Infantino tsaka mai wuya—-wani babban juyin juya hali wanda bayansa, ikonsa da ya zarce fagen ƙwallon ƙafa na duniya ba zai ƙara dawo lami lafiya ba.

ADVERTISEMENT

Ko ma mene ne ra’ayin mista Infantino, ba abu ne mai sauki a yi watsi da yadda ya nuna sha’awar kusantar shugaba Donald Trump, har ma ya kai ga yin watsi da ka’idojin da suka daɗe suna jagorantar fagen wasan ƙwallon ƙafa. Shugaba Trump, a gefensa, ya karɓi wannan girmamawa ba tare da shakku ba, kamar yadda ya yi a hulɗarsa da firaministan Italiya. Sakamakon nan take, shi ne cewa FIFA da shugabancinta sun mika kansu ga ganin baike daga jama’a tamkar dai wasu “’Yan wasan ban dariya”.

Mista Infantino na iya samun dalilai marasa adadi game da dalilin da ya sa ayyukansa suke da mahimmanci, ko kuma suka zama masu amfani a ƙarshe. Amma waɗannan kurakuran da ya jawo wa kansa—masu kama da jefa kwallo a ragar gidansa—sun lalata amincin FIFA sosai. Abun takaici ga hukumar shi ne cewa, wannan ba kawai tunani ba ne a yanzu, amma gaskiya ce ta haƙiƙa. Har yaushe ne za a tantance zurfin raunin da ya faru, da kuma tsawon lokacin da za a ɗauka kafin a warware, hakan ba abu ne da za a tabbatar da amsarsa cikin sauri ba.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

A gaskiya, sauya sheka daga cika da kwarjini zuwa rugujewar aminci ya riga ya fito fili tun kafin wasan bude fage na gasar cin kofin duniya. An fallasa shi ne a lokacin tattaunawar FIFA da China Media Group’s CCTV kan haƙƙin watsa shirye-shirye. Shekaru uku da suka gabata, FIFA ta nace kan farashin da ba za a iya sassantawa a kansa ba. Amma yayin da gasar ke gabatowa, a ƙarshe ta karɓi kusan dukkan sharuɗɗan da CCTV ta gabatar. Ko da yake an yi izgili ga tawagar ƙwallon ƙafa ta kasar Sin saboda rashin samun gurbi a gasar, amma kafafen yada labaran Sinawa sun samu babbar nasara a wani fagen na yaƙi, inda suka ba FIFA da Mista Infantino masu girman kai darasin da ba za su manta ba.

Lokacin da sakataren koli na FIFA Mattias Grafström ya yi murmushi ga kyamarori yana furta cewa, “tattaunawarmu da CCTV ta yi matuƙar nasara. Sakamako ne na cin moriyar juna”, yanayin fuskarsa ya nuna rashin kwanciyar hankali, tare da rahotannin kafafen yada labaru na duniya, da ke nuna ƙarshen da kowa ya yarda da shi: FIFA a ƙarshe ta ja baya a tattaunawar da ta yi da bangaren Sin. Wani ƙalubale daban kuma, shi ne yayin da aka fara gudanar da gasar cin kofin duniya, inuwar da rashin nasarar tattaunawar haƙƙin watsa shirye-shiryen ta bari a jikin FIFA ta tabbata. Yawancin kura-kuran da Mista Infantino ya yi daga baya sun ƙarfafa wannan tunanin.

Babu wanda zai musanta gagarumar gudunmawar da Mista Infantino ya bayar ga FIFA a cikin shekaru goma da suka gabata, musamman kokarinsa na faɗaɗa kimar kasuwanci na wasan. Ko da yake, a idon Shugaba Trump, watakila bai ma cancanci matsayin ɗalibi ba, rashin fahimtar karfin Sin a yau yana nuna irin kuskuren da ya yi game da duniyar yau.

Wayewar yamma ta kan yi amfani da shahararriyar maganar Socrates, “Ka san kanka” a matsayin ka’idar tunani. Amma shugabannin FIFA sun kasa fahimtar babban sauyi da ke faruwa a duniyar yau, ko kuma fahimtar yadda FIFA da kanta ya kamata ta amsa wannan sauyi.

Abin ban dariya shi ne, ba da daɗewa ba bayan da FIFA ta tilasta sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar watsa shirye-shirye tare da CCTV, sakonnin gaisuwa suka iso ga shugaban China Media Group daga shugaban Ligue 1, da shugaban kulob din Paris Saint-Germain, har ma da shugaban kwamitin Olympics na duniya. Bayanan da ake da su a bainar jama’a sun nuna cewa, yayin da waɗannan ƙungiyoyin wasanni na duniya suka taya CCTV murnar samun haƙƙin watsa shirye-shiryen gasar, sun fi mayar da hankali kan nuna fatansu na ƙara haɓaka haɗin gwiwa tare da Ligue 1, Paris Saint-Germain, da IOC. Wannan watakila ba nuna murna ga rashin sa’ar FIFA ba ne, amma tabbas yana nuna cewa tasirin da ƙarfin tattaunawa na kafafen yada labaran Sin suke da shi ya ƙaru sosai.

Alal hakika, ba za a iya kwatanta tattaunawar FIFA da CCTV a matsayin cikakkiyar shan kashi ba, tun da duka ɓangarorin biyu a ƙarshe sun bayyana yarjejeniyar a matsayin mai amfani ga kowa. Duk da haka, raina abokin tattaunawa, da raina abokin hulɗa ya wuce darasi ga FIFA da Mista Infantino su kadai, maimakon haka darasi ne ga duniyar Yamma gaba ɗaya.

Lokacin da motocin lantarki na Sin suka fara shahara a duniya, mutane da yawa a Yamma sun rika yi musu izgili da cewa, “Tarkacen ƙarafa ne kawai marsa tashoshin caji.” Lokacin da mutum-mutumi na Sin suka burge masu kallo yayin bikin Sabuwar Shekara ta Spring Festival Gala, masu sharhi na Yamma cikin tabbaci, sun yi watsi da wasan a matsayin “dabarun AI kawai.” Sai bayan da gaskiya ta ci gaba da tabbata suka tabbatar da kuskurensu, har ma yawancin waɗannan ƙwararru da suke ikirarin ilimi suka rasa karfin gwiwa kan tsinkayensu, inda wasu ma suka fara nuna alamun damuwa.

Ta wani hangen nesa, ƙididdigar da FIFA ta yi game da haƙƙin watsa shirye-shiryen gasar cin kofin duniya, ana iya ganinta a matsayin wani ɓangare na kuskuren Yamma game da Sin a wannan sabon zamani. Raguwar karfin mulkin Yamma bai faru kwatsam ba: ya fara bayyana ne tun shekaru da yawa, ko da yake mutane da yawa a al’ummar Yamma har yanzu ba sa son yarda da hakan.

A zahiri, idan mutane sun yi aiki da hankali, sun tantance bunkasar Sin cikin adalci, kana sun yi mu’amala da Sin a matsayin abokiyar tafiya, kuma sun bi wannan sabuwar abokiyar tattaunawa mai zaman kanta da adalci, damar haɗin gwiwa mai amfani, za a cimma nasarar cin gajiyar bai daya da hadin gwiwa marar iyaka. Yin imani da makomar Sin yana nufin yin imani da makomarmu ta mu’amala. Bayan dukkanin abun da ya auku, shin a karshe ba a cimma yarjejeniyar watsa shirye-shiryen gasar ba?

Wannan, hakika, sabon zamani. (Masu fassarawa: Sanusi Chen, Saminu Alhassan)

Infantino
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
Infantino
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

MASU ALAKA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Next Post
Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.