ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wane Tsarin Kungiyar SCO Ta Ginu A Kai Cikin Shekaru 25?

by Sulaiman
1 week ago
SCO

A daidai lokacin da ake gudanar da taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), daga yau 31 ga watan Agustan zuwa gobe 1 ga watan Satumba a kasar Kyrgyzstan, kungiyar na cika shekaru 25 da kafuwa.Shin wane tsarin kungiyar ta ginu a kai cikin shekaru 25 da ya sa take habaka da samun ci gaba? Babban abun da wannan kungiya wadda kasashe 6 suka fara kafa ta ta ginu a kai shi ne, girmama dukkannin kasashe, watau dukkannin kasashe masu cin gashin kansu, daidai suke da juna babu uban gida da dan gida.

Haka kuma babu raini ko rashin girmamawa. Hakika, kafuwar wannan kungiya ta kalubalanci tsarin hukumomin yammacin duniya inda kasashen ke cudanya da mu’amala ba tare da zama karkashin ikon wata kasa ba. Kungiyar wadda ta bunkasa zuwa kasashe mambobi 10 da suka hada da Sin da Rasha da Kazakhstan da Kyrgyzstan da Tajikistan da Uzbekistan da India da Pakistan da Iran da Belarus, shaida ce mai wakiltar tsarin inganta shugabancin duniya mai girmama cikakken ikon kasashe da babu tsoma baki ko katsalandan, wadda ke kokarin tabbatar da rarrabuwar iko tsakanin kasashe.

Lallai irin wannan hadin gwiwa ake bukata a duniya domin kowace kasa ta bambanta, don haka ita ce mafi dacewa ta zabarwa kanta hanya da dabarun raya kanta da al’ummarta, maimakon kwaikwayo da zama ’yar amshin shata. Wannan ya haifar da dimbin alfanu ga kungiyar inda hadin gwiwa ta moriyar juna da taimakekeniya da ake yi tsakanin kasashen ya sa suke iya gudanar da harkokin cinikayya cikin takardun kudadensu.

ADVERTISEMENT

Lamarin da ya saukaka harkokin cinikayya tare da nuna cewa, bai zama wajibi duniya ta dogara da takardar kudin wata kasa guda ba, sannan shaida ce cewa, duniya na bukatar wani tsarin hadin gwiwa mai martaba kowa da tabbatar da adalci da daidaito da cin moriya tare.

Duk da cewa kasashe ne masu mabambantan tsare-tsare da al’adu da ma yanayi, sun jure kalubale da yanayin duniya, inda suka kasance tsintsiya madaurinki daya, masu ingiza ci gaban juna da goyon bayan juna.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Lamarin da ke kara tabbatar da cewa, rarrabuwar iko da daidaito da samun ci gaba tare, ba za su taba zama kalubale ga ci gaban duniya ba, sai ma karfin da zai ingiza dunkulewar duniyar wuri guda. (Fa’iza Mustapha)

SCO
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

Next Post
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Da Ke Halartar Taron Kolin SCO

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.