• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Halayen Da Maza Ke Nuna Wa Uwargida In Sun Shirya Karin Aure

by Amina Usman
3 years ago
Uwargida

Kamar yadda aka sani aure wani nau’i ne na ibada wanda yake haifar da nishadi natsuwa da jin dadi. Idan aka ce aure ana nufin sadaukarwa da kuma girmama juna.

Zamantakewar aure abu ne da aka gina shi a kan abubuwa biyu zuwa uku na farko akwai kishin juna na biyu akwai yarda da amana. Idan muka dauki yarda da amana zamu ga cewa wani abu ne da ma’auratan biyu suka damkawa junansu inda zamu ga cewa miji yana kokarin kare duk wani martaba na matarsa haka itama matar.

  • Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
  • Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC

Idan muka yi dubi da shimfidan da na fara zamu ga cewa an gina zaman aure a kan turaban sadaukarwa da amana, idan kuwa haka ne to me yasa Miji ke juya wa uwargida baya a lokacin da yake kokarin karo aure?

Yawanci maza in sun yi shirin karin aure gaskiya akwai halayya iri daban-daban da uwargida ke cin karo da su a wurin Maigida ,wanda zamu ga cewa gaba daya miji yakan manta irin zaman dadi da kuma zaman hakuri da ta yi da shi.

Hakazalika miji yana sauyawa ta halayya daban-daban ga uwargida inda har wani lokaci in ba a kai zuciya nesa ba saki ko sabani mai karfi na iya shiga tsakani. Yawanci maza in sun zo karin aure sukan sauya fuska da walwala wa uwargida wanda hakan an yi ittifakin cewa yawanci maza suna ganin cewa si yanzu ita uwargida ta ragwaba bata da sauran mamora shiyasa idon su sai ya kyalla ya fara hango musu wata a waje,wanda har zai kai ga ana diban lokacin uwargida ana baiwa amarya tun kafin ta shigo gidan.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Wani lokaci zakaga idan miji ya fara shirin karin aure zai dauko wasu sababbin halayya wanda uwargida bata sansu ba ya dorawa kansa, kamar misali akwai mijin da zakaga idan yaso karin aure to fa uwargida ta shiga uku don komai ta yi ba ta burge shi ba saima hantara da fada da zai dinga yawan yi mata, ko kuma kaga wani mijin in yaso karin aure to ya daina shiga harkan uwargida musamman da muke da kafafen soshiyal media daban-daban to gaba daya lokacin shi ya zama na amarya ko yaushe suna manne a waya ko kuma suna ‘Charting’ ita uwargida an ajiyeta a gefe an gama yayin ta.

Wani namijin in yaso aure kuma yarasa wani laifi zai mannawa uwargida in aka dameshi da tamabaya wani sai yace ai bata iya tarban baki ba ne saboda a tunanin sa yana ganin kamar ita wacce yake kokarin aurowar tafi kowa hankali ta iya komai dari bisa dari bai san cewa hangen dala yake yi ba. Wani namijin kuwa sababbin halayensa basa chanzawa sai ya auro ta ya kawo cikin gida daga nan ne labari zai chanza salo in ya hadu da itama amaryar ‘yar garice sai su hada kai da mijin su muzgunawa uwargida, misali akwai gidan da za kaga daga ranar da amarya ta zo to fa baban maganar wanda miji zai saurara akwai gidan da naga amarya ta yi wa uwargida sharrin cewa tana bin malamai saboda tana gane ganecin tana bacci irin wannan sharrin kamata ya yi ace mijin ya yi hukunci mai karfi amma abin mamaki sai ya goyi bayan amarya a kan cewa ya yarda uwargida na bin boka. Mai yasa, duk tsawon shekarun da suka yi da uwargidan bai fada mata tana bin malamai ba saida ya karo aure, abubuwa makamantan haka suna faruwa a gidajen aure daban daban a duk sanda miji ya dau kdamaran karo aure.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Motsa Jiki Na Hana Kamuwa Da Muggan Cututtuka -WHO

Motsa Jiki Na Hana Kamuwa Da Muggan Cututtuka -WHO

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

October 24, 2025
Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

October 24, 2025
Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya

Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya

October 24, 2025
Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

October 23, 2025
Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

October 23, 2025
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

October 23, 2025
Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

October 23, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

October 23, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka

October 23, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.