ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, October 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi: Ya Dace A Dauki Matakan Zahiri Don Tabbatar Da Kyakkyawar Dangantakar Sin Da Amurka Mai Gudana Bisa Daidaiton Manyan Tsare-tsare

by CGTN Hausa
1 month ago
Xi

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, sun yi shawarwari a fadar White House da safiyar ranar 24 ga watan nan.
A tattaunawarsu, shugaba Xi ya ce, sabon matsayin dangantakar Sin da Amurka, wato kyakkyawar dangantakar Sin da Amurka mai gudana bisa daidaiton manyan tsare-tsare, ta shaida ainihin halin da ake ciki na raya alakokinsu, tare da nuna kyakkyawan fata a nan gaba, kana muhimmin ci gaba ne da aka samu wajen bin hanya madaidaiciya ta raya dangantakar kasashen biyu. Ya ce ya dace bangarorin biyu su dauki matakai na zahiri don aiwatar da wannnan kyakkyawan fata, a wani kokari na kirkiro kyakkyawar makomar dangantakar Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, matsayin kasar Sin a bayyane yake wajen kiyaye dinkuwarta da cikakken yankinta, tare da fatan Amurka za ta tsaya ga matsayin adawa da yunkurin balle Taiwan daga cikin kasar Sin, da yin tunani mai zurfi game da batun da ya shafi Taiwan, a wani kokari na aza tubali mai inganci ga hadin gwiwar Sin da Amurka bisa manyan tsare-tsare gami da ci gaban dangantakarsu yadda ya kamata.
A daya bangaren, game da batun yankin Gabas ta Tsakiya, shugaba Xi ya nuna cewa, Sin tana ganin cewa, ya kamata a mutunta cikakken ’yanci gami da tsaron duk wata kasa, kuma ta dade tana taka muhimmiyar rawa wajen sassauta yanayin rikicin da ake ciki, da karfafa gwiwar bangarori daban-daban don su bi hanyar lumana, tare kuma da ci gaba da yin shawarwari tsakaninsu.
A nasa bangaren kuwa, Donald Trump ya ce, ziyarar shugaba Xi a Amurka a wannan karo, babbar ziyara ce mai ma’ana sosai. Amurka da Sin kasashe ne manya, kuma shi da shugaba Xi aminan juna ne na arziki, wadanda suka kiyaye tuntubar juna. A karkashin jagorancin shugabannin biyu, alakar Amurka da Sin za ta ci gaba da kyautata.
Shugabannin kasashen biyu sun kuma tabbatar da cewa, za su goya wa juna baya wajen gudanar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe membobin kungiyar APEC na shekara ta 2026, gami da taron kolin G20. (Murtala Zhang)

Xi
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu
Daga Birnin Sin

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta
Daga Birnin Sin

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Next Post
Kingsley Moghalu Ya Yi Watsi Da Shiga Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku

Kingsley Moghalu Ya Yi Watsi Da Shiga Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku

LABARAI MASU NASABA

An Fitar Da Matar Da Ta Kamu Da Ebola Daga Nijeriya Zuwa Switzerland

An Fitar Da Matar Da Ta Kamu Da Ebola Daga Nijeriya Zuwa Switzerland

October 26, 2026
Adadin Waɗanda Aka Kashe A Harin Ƴan Bindiga Ya Kai 50  A Taraba

Adadin Waɗanda Aka Kashe A Harin Ƴan Bindiga Ya Kai 50 A Taraba

October 26, 2026
Kano Da Wasu Jahohi 7 Da Ake Hasashen Samun Hazo Yau Litinin – NiMet

Kano Da Wasu Jahohi 7 Da Ake Hasashen Samun Hazo Yau Litinin – NiMet

October 26, 2026
NDC Ta Caccaki Tinubu Da APC Kan Raba Motocin Prado Na Sama Da Biliyan Ɗaya

NDC Ta Caccaki Tinubu Da APC Kan Raba Motocin Prado Na Sama Da Biliyan Ɗaya

October 26, 2026
Akwai Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa Masu Rajista Fiye Da 500 A Kano – Ahlan

Akwai Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa Masu Rajista Fiye Da 500 A Kano – Ahlan

October 26, 2026
INEC Za Ta Yanke Hukunci Kan Takarar Pantami, Gwarzo, Da Adebutu Ranar 29 Ga Oktoba

INEC Za Ta Yanke Hukunci Kan Takarar Pantami, Gwarzo, Da Adebutu Ranar 29 Ga Oktoba

October 26, 2026
Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

October 25, 2026
An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.