Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga al’ummun kasarsa, da su zage damtse cike da kwarin gwiwa, da bin matakai masu kwari na cimma nasarar matakan farfado da kasa.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar Sin, ya yi wannan kira ne a Larabar nan, ciki jawabin da ya gabatar a babban zauren taruwar jama’a dake nan birnin Beijing, yayin liyafar murnar cika shekaru 77 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
Shugaba Xi, ya jaddada cewa ta hanyar shafe tsawon lokaci ana bincike da gwaji, tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta Sin ya shaida muhimmin tasiri da yake da shi. Kazalika, tsarin zamanantarwa na gwamnatin Sin, da ikon jagoranci sun ci gaba da kyautata, kuma cimma nasarar farfado da kasar Sin bisa babban matsayi ya zamo wani kuduri da bai zai sauya ba.
A gobe Alhamis daya ga watan Oktoba ne ake gudanar da bikin cika shekaru 77 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. (Saminu Alhassan)














