Wani mutum mazaunin Jihar Kano, mai suna Ibrahim Yusuf, ya rasa ’ya’yansa biyar cikin kwanaki takwas sakamakon zargin kamuwa da cutar mashaƙo.
Yusuf, wanda ke zaune a unguwar Danbare da ke cikin birnin Kano, ya ce ’ya’yansa sun fara kamuwa da zazzaɓi a makon da ya gabata.
Ya kai su Cibiyar Kiwon Lafiya da ke Kabuga, amma daga baya aka tura su Asibitin Cututtuka Masu Yaɗuwa (IDH) bayan yanayinsu ya tsananta.
Ya ce biyu daga cikin ’ya’yansa sun rasu a ranar Litinin, yayin da sauran ukun suka rasu daga baya biyon alamun irin cutar da ta kashe ‘yan uwansu.
Yaran da rasu sun haɗa da Sadiq, mai shekaru 13; Aisha da Zainab, masu shekaru bakwai-bakwai, Umar mai shekaru shida; da Aliyu, ɗan shekara ɗaya da wata shida.
Mahaifin, wanda yake da ’ya’ya 11, ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar.
Wani ma’aikacin Hukumar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ya tabbatar da mutuwar yaran biyar, inda ya ce adadin mutanen da ke mutuwa a asibitin na ƙaruwa.
Jami’an lafiya sun shawarci mazauna jihar da su yi wa ’ya’yansu allurar rigakafi tare da gaggauta zuwa asibiti idan suka lura da alamun cutar mashaƙo.
Mashaƙo cuta ce mai tsanani da ƙwayoyin cuta ke haddasawa, wadda galibi ta ke shafar hanci da maƙogwaro.
Tana iya yaɗuwa ta ɗigon yawu da ke fita yayin tari ko atishawa, ko kuma kusantar wanda ya kamu da cutar.
Alamomin cutar sun haɗa da zazzabi, ciwon maƙogwaro, wahalar haɗiyar abinci da kuma matsalar numfashi.
A wasu lokuta cutar na iya lalata zuciya da jijiyoyin sadarwa ko kuma ta yi sanadin mutuwar mutum.
Masana kiwon lafiya sun jaddada cewa yin allurar rigakafi, fara shan magani da wuri da kuma killace masu ɗauke da cutar na da matuƙar muhimmanci wajen daƙile yaɗuwarta.














