ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Karyata Maganar Wai Akwai “Matsin Kasar Sin”

by Sulaiman and Bello Wang
2 months ago
Sin

Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Mike Pompeo, ya taba bayyana salon Amurka na tsoma baki a harkokin duniya da cewa, “Muna yin karya, muna yaudara, muna kuma sata.” Ya ce, “Hakan ya nuna halayyar kasar Amurka mai alfahari yayin neman ci gaba.” Bari mu tuna da wannan magana, domin da gaske ita ce ka’idar da kasar Amurka take bi, yayin da take gabatar da maganganu da aiwatar da ayyuka daban daban.

A kwanan baya, wata cibiyar nazari ta kasar Amurka, wato “Peterson Institute for International Economics” ta fitar da wani rahoto mai kunshe da sabon ra’ayi na wai “matsin kasar Sin”, wai masana’antun kasar Sin ba ma kawai suna haifar da matsin lamba ga bangaren hada kayayyaki na Turai da Amurka ba, har ma suna matsawa masana’antun sauran kasashe masu tasowa. Wannan sabon ra’ayi, an kirkiro shi ne bisa tushen laifin da kasashen yamma suka dora wa kasar Sin wai kasar na “samar da kayayyaki fiye da kima”, sai dai ra’ayin da aka gabatar a wannan karo ya nuna niyyar haifar da rashin jituwa tsakanin kasashe masu tasowa.

Amma, yadda Amurka ke kokarin shafa wa kasar Sin bakin fenti wani abu ne da har Amurkawa da kansu ba za su yarda da shi ba. Misali, Lawrence Freeman, wani mai sharhi kan harkokin siyasa da tattalin arziki dan kasar Amurka, wanda ya kware a fannin nazarin manufofin tattalin arzikin kasashen Afirka, ya rubuta wani bayani a kwanan nan, inda ya bayyana cewa mutanen da suka kirkiro ra’ayin “matsin kasar Sin” sam ba su da gaskiya.

ADVERTISEMENT

Lawrence Freeman ya ce, bisa ra’ayin “matsin kasar Sin”, ana ikirarin cewa “rarar cinikayyar kasar Sin tana gurtunta masana’antun kasar Amurka”. Sai dai maganar ba ta da tushe. A cewar Freeman, Amurka ta fara durkusa bangarenta na hada kayayyaki da kanta tun a farkon shekarun 1980. A wancan lokacin, Amurka ta nemi kafa wata al’umma maras dogaro kan masana’antu a cikin gidanta, inda ta fara rufe galibin masana’antu, ban da masu hada makamai da sauran kayayyaki masu kunshe da fasahohin zamani. Ban da haka, kasar ta zama cibiyar hada-hadar kudi, gami da kokarin raya bangaren samar da hidimomi.

Yayin da a nata bangare, kasar Sin ba ta samu cikakken karfi a fannin masana’antu ba a lokacin.Dangane da ikirarin cewa wai “kasar Sin tana tare hanyar sauran kasashe masu tasowa a fannin raya masana’antu”, mista Freeman ya dauki nahiyar Afirka a matsayin misali, yana mai cewa, alal hakika kasar Amurka da sauran kasashen yamma ne ke da alhakin haddasa koma baya a kasashen Afirka ta fuskar masana’antu. A cewarsa, tun daga shekarun 1940 har zuwa lokacin da kasar Sin ta fara zama kasa mai karfin tattalin arziki a shekarar 2000, tsarin tattalin arzikin duniya ya dade yana karkashin jagorancin kasar Amurka da sauran kasashen dake yammacin duniya. Su ne, maimakon kasar Sin, ke da alhakin gaza tabbatar da ci gaban tattalin arziki a dimbin kasashe masu rauni, cikin tsawon shekaru 60.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Dalilin da ya sa haka, a cewar mista Freeman, shi ne “manufofin kasashen yamma ba su taba kunsar niyyar shigar da kasashen Afirka cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya ba.” Akasin haka, kasar Sin, ta hanyar aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI), ta gina dimbin ababen more rayuwa a kasashe daban daban, wadanda suka kasance tushen bunkasa masana’antu.

Mista Freeman ya kara da cewa, “Da babu shawarar BRI, da yanayin rayuwar yawancin mutanen kasashen Afirka ya fi muni.”Za a iya daukar sabon ra’ayin da bangaren Amurka ya kirkira a wannan karo a matsayin wani matakin da ya bayyana niyyar kasar ta hana kasar Sin samun ci gaba. Sai dai duk wata maganar da kasar Amurka za ta fada, ba za ta karkata hankalinmu daga tunawa da zancen mista Mike Pompeo da ya shafi “halayyar kasar Amurka mai alfahari” ba. (Bello Wang)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Sin
Bello Wang
+ posts Bio
  • Bello Wang
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-wang/
    Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Dama Ce Ga Kasashen Afirka

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Hisbah

Rajistar Shirin Auren Gata Na Kano Kyauta Ce, In Ji Hukumar Hisbah

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.