ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Ra’ayin Duniya Ke Karkata Zuwa Sin Yayin da Tasirin Amurka Ke Faduwa?

by Sulaiman
2 months ago
Amurka

Sabon binciken ra’ayin jama’a na duniya da Cibiyar Bincike ta “Pew Research Center” ta fitar ya wuce batun tarin alkaluma kawai. Binciken tamkar madubi ne da ke nuna yadda tunanin al’ummomin duniya ke sauyawa da kuma yadda sabon tsarin duniya ke kunno kai. Tsawon shekaru da dama, Amurka ce ta mamaye matsayin jagorar duniya ta fuskar siyasa, tattalin arziki. Amma a yau, alamu na nuna cewa mutane da dama a sassa daban-daban na duniya sun fara karkata hankalinsu zuwa Kasar Sin.

Binciken, wanda ya gudana a kasashe da yankuna 36, ya nuna cewa Sin ta samu karbuwa fiye da Amurka a sassa masu yawa na duniya. Shekaru uku kacal da suka gabata, Amurka ce ke kan gaba sosai wajen samun amincewar jama’ar duniya. Yanzu kuwa wannan rinjaye ya dusashe. Irin wannan sauyi mai girma ba za a iya danganta shi da sauyin ra’ayin jama’a na dan lokaci kawai ba. A’a, yana nuna cewa duniya ta fara sake nazarin yadda kasashe ke amfani da karfinsu, yadda suke gina hadin gwiwa da kuma yadda suke amsa bukatun duniya.

Babu wata wahala a fahimci dalilin wannan sauyi. A yawancin kasashen Afirka, Asiya, Gabas ta Tsakiya da Latin Amurka, kasashen sun fi yarda da ganin aikin habaka ababen more rayuwa kan ci gaba mai amfani a fili fiye da wa’azin baka. Don haka, tambayoyin da jama’ar ke yi, sun fi zama na zahiri: Wa ke gina tituna, layukan dogo da tashoshin jiragen ruwa? Wa ke saka jari a makamashi, fasaha da bunƙasa masana’antu? Wa ke ba da damar ci gaban tattalin arziki ba tare da dora sharuddan siyasa ba? A idon kasashe masu tasowa da dama, Sin na ƙara ba da amsoshi masu gamsarwa ga wadannan tambayoyi.

ADVERTISEMENT

Shirin Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) na Sin ya zama daya daga cikin manyan shirye-shiryen raya kasa na duniya a wannan zamani, inda ya hada kasashe sama da 150 ta hanyar zuba jari da gina manyan ayyukan more rayuwa. Duk da cewa masu suka na ci gaba da nuna damuwa kan wasu fannoni na shirin, masu goyon bayansa suna ganin ayyuka a fili inda suke nuni da sabbin tituna, layukan dogo, tashoshin samar da wutar lantarki, yankunan masana’antu da inganta harkokin kasuwanci da suka taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasashe da dama. Ga miliyoyin mutane, wadannan ba dabarun siyasar kasa da kasa ba ne kawai, illa ci gaba ne da suke gani da idonsu a rayuwarsu ta yau da kullum.

Haka kuma, Sin ta kafa kanta a matsayin daya daga cikin jagororin duniya a sabbin fasahohi. Daga motocin lantarki da makamashi mai tsafta zuwa kirkirar basirar dan’Adam (AI) da fasahar sadarwar 5G, Sin ta tabbatar cewa kirkire-kirkire ba mallakin kasashen Yamma kadai ba ne. Mafi muhimmanci, ta nuna shirinta na raba wadannan fasahohi da kasashe masu tasowa ba tare da dora musu irin sharuddan siyasa da galibi ke tattare da tallafin kasashen Yamma ba.

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

A fagen diflomasiyya kuma, Sin ta yi kokarin gina sunanta a matsayin kasar da ta fi fifita tattaunawa fiye da tayar da tarzoma da yake-yake. Ta hanyar shirye-shirye irin su “Global Development Initiative, Global Security Initiative da Global Civilization Initiative”, Sin na ci gaba da gabatar da kanta a matsayin mai goyon bayan hadin gwiwar kasa da kasa da ci gaba cikin lumana.

A gefe guda kuma, martabar Amurka a idon duniya ta samu koma baya sakamakon wasu manufofinta da dama. Kara amfani da takunkumai, harajin kwastam na rashin tunani, yake-yaken kasuwanci da matsin lambar siyasa, ya sa mutane da dama suna tambayar ko har yanzu Washington na bin ka’idojin tsarin duniya da ita kanta ta dade tana kira a kansu. Har ma tsakanin Amurka da manyan kawayenta a Turai da Arewacin Amurka, sabanin ra’ayi da tsamin danganta kan harkokin kasuwanci, makamashi, fasaha da ‘yancin yanke shawara ya fara bayyana karara.

Ana danganta Sin da gina ababen more rayuwa, bunkasa masana’antu da saka hannun jari. A gefe guda kuma, galibi ana kallon Amurka ta fuskar buga takunkumai, kutse ta hanyar soji da kuma gogayyar siyasa tsakanin manyan kasashe.

Sakon da sabon binciken ya fito da shi a bayyane yake. Ka’idojin da ake amfani da su wajen auna tasirin kasashe ya fara canzawa. Ƙarfin soja ko tasirin kasa ba su ne ke tabbatar da mutunta wannan kasar kai tsaye ba. A maimakon haka, an fara auna kasashe ne da irin gudummawar da suke bayarwa wajen samar da ci gaba, karfafa hadin gwiwa, mutunta ikon kasashe da kuma inganta rayuwar talakawa.

Tarihi ya koya mana cewa babu wata kasa da za ta ci gaba da rike jagorancin duniya har abada. Kowace babbar kasa dole ne ta ci gaba da neman amincewa da girmamawar al’ummomin duniya. Kuma a halin yanzu, wannan amincewa na ci gaba da karkata zuwa ga Sin.

Amurka
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya
  • Sulaiman
    An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu
  • Sulaiman
    Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa
  • Sulaiman
    Nazarin CGTN: Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Nuna Kudurin Sin Na Bunkasa Bude Kofa

MASU ALAKA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka
Ra'ayi Riga

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Next Post
Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu’ar Roƙon Ruwa A Azare

Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu'ar Roƙon Ruwa A Azare

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

September 17, 2026
U-20: Nijeriya Ta Doke Ingila Da Ci 3-0, Ta Kai Zagayen Kwata-fainal

U-20: Nijeriya Ta Doke Ingila Da Ci 3-0, Ta Kai Zagayen Kwata-fainal

September 17, 2026
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu

September 17, 2026
Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa

Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa

September 17, 2026
Nazarin CGTN: Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Nuna Kudurin Sin Na Bunkasa Bude Kofa

Nazarin CGTN: Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Nuna Kudurin Sin Na Bunkasa Bude Kofa

September 17, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Sin Da ASEAN Na 23

An Kammala Taro Na 13 Na Dandalin Tattauna Tsaro Na Xiangshan A Beijing

September 17, 2026
Ka Da Ku Siyar Da Gidajenku Don Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote – Sanusi II

Ka Da Ku Siyar Da Gidajenku Don Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote – Sanusi II

September 17, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Sin Da ASEAN Na 23

Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Sin Da ASEAN Na 23

September 17, 2026
Lalong Da Uwargidan Shugaban Ƙasa Sun Goyi Bayan Ci Gaban Sauye-Sauyen Tinubu

Lalong Da Uwargidan Shugaban Ƙasa Sun Goyi Bayan Ci Gaban Sauye-Sauyen Tinubu

September 17, 2026
Fitar Da Shirin Shekaru 5 Ya Bude Sabo Babi Na Tsarin Ci Gaban Yankin HK

Fitar Da Shirin Shekaru 5 Ya Bude Sabo Babi Na Tsarin Ci Gaban Yankin HK

September 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.