Me zai iya faruwa cikin tsawon rabin shekara?
Ga avokado na Kenya, ya zamanto daga ‘ya’yan itace a ressan bishiyoyi zuwa kaya mai matukar karbuwa a cikin manyan shagunan kasar Sin. Ga ‘yan kasuwar fitar da ridi na Najeriya kuma, rabin shekara ya shaida yadda harajin ridin da ake fitarwa zuwa Sin ya sauko daga kashi 10 cikin dari kai-tsaye zuwa sifiri, matakin da ya sa kudin da aka biya na shigo da shi ya ragu da sama da dala dubu 10 a kan kayan tan 100.
A ranar 1 ga Mayun 2026, Sin ta fara aiwatar da manufar soke gaba dayan harajin kwastam kan kayayyakin dukkanin kasashen Afirka 53 masu dangantakar diflomasiyya da ita. Sama da rabin shekara ke nan da aiwatar da wannan manufa. Gobe kuma, za a kaddamar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) karo na tara. In an ce manufar soke haraji ta bude kofar shigo kasuwar kasar Sin ga kayayyakin Afirka, to, bikin CIIE ya samar da dandali na hada ‘yan kasuwar kasar Sin da takwarorinsu na Afirka ke nan.
Soke haraji bai tsaya ga manufa ba, a maimakon hakan, ya zamanto karuwar kayayyakin da kasashen Afirka suke fitarwa da kuma riba mai tsoka da kamfanoninsu suke ci. Alkaluman hukumar kwastam ta Shenzhen da ke kudancin kasar Sin sun nuna cewa: cikin rabin shekarar da ta wuce, an shigo da rukunonin kaya 2424 daga kasashe 20 na Afirka da ke da dangantakar diflomasiyya da kasar Sin, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan miliyan 799, inda aka rage haraji sama da yuan miliyan 71. Harajin shigo da ‘ya’yan itace da ake kira “grapefruit” a Turance ya sauko daga kashi 12% zuwa sifiri, wanda hakan ya rage kudin da ‘yan kasuwar shigo da kaya suke biya tare da karfafa musu gwiwar habaka shigowa da kayan.
Alfanun manufar ba ta tsaya kan hakan ba kawai, duba da cewa yadda ake hasashen karuwar kayayyakin da kasashen Afirka ke fitarwa zuwa kasar Sin zai jawo hankulan masu zuba jari na cikin gida da waje zuwa fannonin noma, sarrafa abinci da sarrafa ma’adanai a kasashen Afirka kamar Najeriya.
Sarrafa kayayyaki a cikin gida don kara darajarsu kafin daga bisani a fitar da su zuwa kasuwar Sin, zai taimaka wajen fadada tsarin samar da kayayyaki a kasashen Afirka, tare da sa kaimin bunkasar fannonin nazari da kirkire-kirkiren kayayyaki da gwajin ingancinsu da kunsa kayayyaki da ajiye su da jigilarsu, wanda zai sa kasashen Afirka su canza daga fitar da danyun kayayyaki zuwa fitar da kayayyakin da aka sarrafa, tare da kara karfin tattalin arzikinsu.
Kamar yadda darektan Cibiyar Nazarin Sin ta Najeriya, Charles Onunaiju ya ce, “Ba gudummawa kadai kasar Sin ta samar ba, a’a, tana taimaka wa kasashen Afirka su samu canji ta hanyar samar da kayayyaki da kasuwanci da ci gaban masana’antu.”Ko da yake manufar soke haraji ta bude kofar shigo kasuwar kasar Sin ga kayayyakin kasashen Afirka, amma da gaske kamfanonin Afirka za su iya fitar da kayayyakinsu kuma a kan farashi mai gamsarwa? To, bikin CIIE ya samar da amsa bisa dandalin da ya bayar ke nan.
Bikin na bana ya kasance na farko tun bayan da kasar Sin ta fadada manufar soke haraji zuwa gaba dayan kasashen Afirka 53 da ke da dangantakar diflomasiyya da ita, kuma kamfanoni da yawa na Afirka sun shirya zuwa Shanghai da kayayyakinsu masu inganci, don fatan ganin ta hanyar baje kolin su sami abokan ciniki da kuma kasuwa. In mun duba, a bana Tanzaniya ta tura kamfanoni da hukumomi 36, yayin da a shekarar 2021 wannan adadin ya kasance 6 kawai.
Har ila yau, Bankin Standard na Afirka ta Kudu ya kawo kamfanonin noma da sarrafa kayayyakin gona na Afirka 20 gaba daya, kuma kayayyakin da za su nuna sun hada da kofi, da koko, da avokado, da kyashu, da ridi da sauransu. A bana, bikin CIIE ya kuma inganta sashin nuna kayayyakin Asiya da Afirka na musamman, don taimaka wa kasashen Afirka su yi amfani da damar da manufar soke haraji ta kawo.
To, ke nan bayan da aka bude kofar shigo kasuwar kasar Sin tare da kafa dandalin hada ‘yan kasuwar sassan biyu, “nesa ta zo kusa” ke nan ga kayayyakin Afirka, haka nan ga al’ummar kasar Sin masu saye.
Idan za mu yi tsokaci a kan manufar soke haraji da kasar Sin ta aiwatar, da ma bikin CIIE a daidai wannan lokacin da ake cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, a zahiri za mu ce suna amsa wata tambaya, wato yayin da ra’ayin kashin kai da kariyar ciniki ke kunno kai, me zai faru idan Sin ta kara bude babbar kasuwarta ga ‘yan uwanta kasashen Afirka? Ga shi furannin Afirka sun shiga kasuwannin fure na kasar Sin, kuma ana ta tallata kofi na Ruwanda ta kafofin sayar da kaya ta yanar gizo a kasar, inda hakan ke haifar da ci gaban kasashen Afirka da kyautata jin dadin rayuwar al’ummominsu.














