Zamanantar da masana’antu, da amfani da sabbin fasahohin zamani da kuma inganta hanyoyin samar da kayayyaki, na daga cikin manyan abubuwan da ke taimaka wa kasar Sin wajen bunkasa tattalin arzikinta. Na shaida wannan da idona yayin ziyarar da muka kai wasu kamfanoni biyu a lardin Hunan na kasar kwanan nan. Daya na kera kyastu (lighter), dayan kuma na sarrafa awara ko “doufu” da Sinanci.
A kamfanin kera kyastu da ke birnin Shaoyang, na ga yadda kamfanin ya rungumi fasahar zamani wajen samar da kayayyaki masu inganci. Kamfanin, wanda aka kafa shekaru 17 da suka gabata, yana da sassan samar da kayayyaki masu amfani da na’urori na zamani, wadanda ke aiki ba dare ba rana.
Haka kuma, yana da sassan da ma’aikata ne kawai ke gudanar da ayyukansu kai-tsaye.
Kamfanin yana da ma’aikata kusan 3,100, da kuma injiniyoyi 32 da ke gudanar da bincike da nazari domin inganta kayayyakin da yake samarwa har ma da kirkiro sababbi, inda ake bin matakai 12 wajen kera kyastun, da kuma matakai 15 na tantance ingancinsu kafin fitarwa kasuwa.
A lokacin ziyararmu, kamfanin yana samar da manyan nau’o’in kyastu guda takwas, wadanda ake kaiwa kasashe da yankuna sama da 180 a duniya. A halin yanzu ma, kamfanin ya ce yana samar da kyastu mai amfani da batir, wanda ya dace da ka’idojin tafiya da shi a jirgin sama. Haka kuma, kamfanin ne ke samar da kyastun AK da ake da amfani da shi sosai a Nijeriya da ma wasu sassan Afirka.
An bayyana mana cewa kamfanin yana taka muhimmiyar rawa a kasuwar duniya. Kuma wani abin sha’awa shi ne, duk da hauhawar farashin kayayyaki a duniya, kamfanin yana ci gaba da samar da kyastu masu araha ba tare da kara farashi ba tsawon kusan shekaru 20, wanda hakan ba zai rasa nasaba da irin goyon bayan da yake samu daga gwamnatin birnin Shaoyang da ta lardin Hunan ba.
A daya bangaren kuma, ziyararmu a kamfanin sarrafa awara da ke Wugang, ta ba mu damar ganin yadda ake amfani da fasahar zamani wajen samar da abinci mai dadin dandano. Kamfanin yana da ma’aikata kusan 1,000, da rassa biyu da ke tsakanin juna da tazarar da ba ta wuce kilomita biyar ba.Mun zagaya sassa daban-daban na kamfanin, ciki har da dakin gwaje-gwaje, da sashen hada kayan yaji, da sashen zuba miya ko garin dandano da kuma wuraren kunshe awarar.
Kamfanin yana samar da nau’o’in awara masu dandano daban-daban, baya ga sauran kayayyakin abinci kamar gasasshen naman agwagwa, yayin da yawan awarar da yake samarwa a shekara tana iya kaiwa kusan tan 30,000. Haka kuma, kudaden shigar da yake samu daga awarar a shekara, suna kaiwa tsakanin Yuan miliyan 700 zuwa 800.
Abin da ya fi daukar hankalina a ziyarar kamfanonin biyu shi ne yadda suke kokarin zamanantar da kansu da kuma fadada cinikayyarsu. Kazalika, wannan darasi ne da ya kamata kasashe masu tasowa su dauka wajen bunkasa tattalin arzikinsu da abubuwan da suke da su ba tare da renawa ba.
Wasu da yawa za su iya daukar kyastu da awara a matsayin wasu kananan abubuwa, amma kuma a duba yadda kasar Sin ta ba su muhimmanci har suke samar da ayyukan yi da samun kudaden shiga masu yawa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













