Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro, farfaɗo da fatan ’yan Nijeriya da kuma rage tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan isa Jihar Sokoto domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya gode wa magoya bayan da suka tarbe shi, yana mai cewa ’yan Nijeriya sun gaji da yunwa, rashin tsaro da kuma alƙawuran da ba a cikawa.
Ya ce zai mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar al’umma, dawo da fata ga matasa da kuma samar da yanayin rayuwa mai sauƙi.
Atiku ya bayyana ƙaddamar da kamfen ɗin a Sokoto a matsayin farkon tafiyar da ya ce za ta kawo sauyi a ƙasar, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa kan nasarar ADC a zaɓen 2027.
Zuwansa Sokoto ya biyo bayan zargin da ya yi a ranar da ta gabata cewa Hukumar DSS na ƙoƙarin kawo cikas ga kamfen ɗin jam’iyyarsa a jihar.














