Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, a watanni 9 na farkon bana, jimillar cinikayyar shige da fice kan harkokin ba da hidima na Sin ta wuce kudin Sin yuan triliyan 5.76, wadda ta karu da kashi 8.5 cikin kashi 100, idan an kwatanta da ta makamancin lokaci na shekarar da ta gabata.
Bayanan sun nuna cewa, a wadannan lokuta, yawan hidimomin da Sin ta fitar ya kai sama da yuan triliyan 2.27, wanda ya karu da kashi 14.8 cikin kashi 100 a mizanin shekara-shekara, yayin da yawan shigo da hidimomi ya haura yuan triliyan 3.49, wanda ya karu da kashi 4.8 cikin kashi 100 a mizanin shekara-shekara.
Gibin cinikayyar hidimomi ya kai kimanin yuan triliyan 1.23, wanda ya ragu da yuan biliyan 132.66 a mizanin shekara-shekara.Saurin bunkasuwar cinikayyar hidimomin sufuri ta fi karuwa wanda ya kai matsayin koli.
A watannin 9 kuma, yawan cinikayyar shige da fice a fannin hidimomin sufuri ta wuce yuan biliyan 128.172, wanda ya karu da kashi 33.9 cikin kashi 100, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar bara.(Amina Xu)














