Rundunar ’yansandan Babban Birnin Tarayya ta kama wani mutum mai suna Zayyanu Halilu bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyaɗe a Abuja.
’Yansanda sun ce jami’ansu sun kama mutumin ne a ranar 2 ga watan Oktoba, yayin da ake zargin yana lalata da yarinyar a cikin wata mota a tashar mota da ke ƙarƙashin gadar hanyar zuwa titin filin jirgin saman Abuja.
Rundunar ta ce daga baya an gano cewa yarinyar tana da ciki na kimanin watanni uku.
Bincike ya kuma nuna cewa ana zargin mutumin ya jima yana lalata da yarinyar tare da yi mata barazanar kada ta sanar da kowa.
A halin yanzu, an kai yarinyar asibiti domin kula da lafiyarta, yayin da wanda ake zargin yake hannun ’yansanda.
’Yansanda sun ce za su gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’yansandan Abuja, Ahmed Muhammed Sanusi, ya yi kira ga iyaye da su riƙa sanya ido sosai kan lafiyar da tsaron ’ya’yansu.














