Jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS tana jagorantar mutane biliyan 14 don samun ci gaba da tinkarar kalubaloli a nan kasar Sin, kuma babban jagorar jam’iyyar shi ne Xi Jinping, wato babban sakataren kwamitin kolin JKS.
Xi Jinping ya gabatar da cikakken jerin tsare-tsaren gudanar da harkokin inganta JKS, wato tunanin Xi kan inganta jam’iyyar. Wannan ka’ida da ya gabatar don magance matsalolin da babbar jam’iyyar ke fuskanta ita ce, dole a daidaita harkokin tawaga mai tafiyar da mulki yadda ya kamata, muddin ana son shugabancin kasa mai kyau, kuma abin da aka sa gaba wajen daidaita harkokin tawaga mai tafiyar da mulki shi ne, sanya muradun jama’a a gaban komai.
Za mu wallafa wani cikakken bayani game da tunanin Xi Jinping kan inganta JKS a shafin musamman na “Binciken Asali da Neman Sanin Gaskiya” dake jaridar Leadership Hausa da za a fitar a Juma’ar makon gobe. (Amina Xu)














