ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Kasar Sin Na Kara Samun Tagomashi A Kasuwannin Duniya

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
default

default

A ’yan shekarun baya bayan nan, duniya na ta ganin karin karbuwar motoci masu aiki da lantarki kirar kasar ko EVs, inda kasuwar irin wadannan motocin fasinja da ake kerawa a kasar Sin ta haura na kamfanonin kirar motoci na kasar Japan a sassa daban daban na duniya.

Wasu alkaluma sun nuna yadda a watan Mayun bana, a karon farko a tarihi sabbin motocin EVs kirar kasar Sin suka mamaye kasuwannin Turai, tare da zarce takwarorinsu na Japan.

Alkaluman sun kuma nuna yadda manyan kamfanoni kirar motoci na farko a tarihin kasar Sin guda biyar, suka sayar da jimillar motoci 138,410 a kasashen Turai 31 a watan na Mayu, adadin da ya karu da kaso 65 bisa dari a mizanin shekara-shekara, yayin da takwarorinsu na Japan guda 6 suka sayar da jimillar motoci 130,424, wanda hakan ke nuna raguwar cinikinsu da kaso 3 bisa dari kan na shekarar bara.

ADVERTISEMENT

Tabbas wannan sabon ci gaba ya ja hankali, ya kuma haifar da tambayar cewa, shin ko me ya sa motoci samfurin EVs kirar kasar Sin suka cimma wannan gagarumar nasara? Amsar ba mai wahala ba ce. Hakan sakamako ne na fifikon fasahohi, da ikon gogayya da kamfanonin kirar motoci na Sin ke da su. Bayan kwashe gomman shekaru ana zuba jari, da gudanar da bincike da gwaje-gwaje, Sin ta gina tsari mai na-garta, da fifiko a manyan fannonin kirar motoci samfurin EVs, musamman fannin kirar batura masu inganci, da na’urorin sarrafa injuna, da fannin kere-keren sauran sassan da ake bukata don hada motocin.

Yayin da fasahohi suka hadu da karfin sarrafa hajoji, aka kuma samu damar rage farashin kaya masu karko, tabbas masu sayayya za su rungumi kasuwar da ta samar da wannan rangwame. Ma iya cewa duk da kalubale da motocin lantarki kirar kasar Sin ke fuskanta a kasuwannin waje, ciki har da karin haraji a wasu sassa, da shingen cinikayya, hakan bai hana su samun karin karbuwa.

LABARAI MASU NASABA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Kuma baya ga na-garta, karko, saukin farashi da suke baiwa masu sayayya, motocin kirar EVs na kasar Sin suna kuma bayar da muhimmiyar gudunmawa ga batun rage fitar da hayaki mai dumama yanayi. Kuma hakan babbar gudunmawa ce ga duniya, musamman ma a wannan gaba da duniya ke dandana kudarta, bisa yanayin zafi dake karuwa sanadiyyar mummunan tasirin sauyin yanayi. (Saminu Alhassan)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Daga Birnin Sin

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
Daga Birnin Sin

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Next Post
Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Hukumomin Tsaro

Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Hukumomin Tsaro

LABARAI MASU NASABA

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Sin

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Sin

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.