Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa makarantun da aka rufe a yankunan da matsalar ’yan bindiga ta yi ƙamari, za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai yanayin tsaro ya inganta.
Gwamnatin ta ce matakin, wanda aka ɗauka kimanin watanni bakwai da suka gabata, ya samo asali ne daga la’akari da yanayin da ake ciki na tsaro kawai, kuma ba za a sake buɗe makarantun ba har sai an tabbatar da tsaron ɗalibai da malamai.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Gwamna Shawara na Musamman kan Sadarwa da Dabaru, Abdullahi Idris, ya fitar a ranar Alhamis.
Acewarsa, “Makarantun da abin ya shafa za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai yanayin tsaro ya ba da damar sake buɗe su cikin aminci. Ba za mu taɓa yin wasa da rayukan ɗalibanmu da malamanmu ba a kowane hali.”













