Shugabar hukumar hana yaduwar cutar kanjamo ta kasa (NACA) DoktaTemitope Ilori, ta ce har yanzu lamarin kokarin da ake yi na hana da, ya dauki cutar daga wurin uwa, da kuma yara wadanda suke dauke da cutar har yanzu abin ya tsaya ne a kashi 33, wato bai kai ga kashi 95 da ake son cimmawa ba.
Da take jawabi da kuma tunawa da rahoton UNAIDS na shekarar 2023, Dokta Ilori ta ce ku san yara 160,000 da suke 0-14 suna rayuwa ne da cutar kan jamo a Nijeriya.
- Tashin Farashin Kayan Masarufi Ya Fi Illa Ga Mazauna Jihohin Sakkwato, Edo Da Borno
- Dalilan Da Suka Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Talauci Duk Da Karuwar Kudin Shiga – Masana
Shugabar ta bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja lokacin taron manema labarai kafin ranar cutar kanjamo ta shekarar 2024, mai taken: “A dauki hanyar da ta dace: Ci gaba da amfani da maganin da ya dace, hana yaduwar cutar HIB tsakanin yara, saboda a kawo karshen cutar nan da shekarar ta 2030”.
Bikin ranar kanjamo ana yin shi ne kowace shekara 1 ga watan Disamba domin a samu wayar da kan al’umma dangane da cutar da kuma kwayar cutar da take sanadiyar ta.
A kan yadda cutar take har ila yau shugabar tace mutane milyan 1.4 ne masu shekaru daga 15 zuwa 64 da akwai mutane milyan biyu da suke rayuwa da cutar a Nijeriya.
Bugu da kari kuma an samu mutane 22,000 da suka kamu da sabuwar cutar HIB sai kuma mutuwar mutane 15,000 a ko wace shekara.
“Nijeriya na da mutane da suka kai kashi 1.4 cikin 100, daga cikin al’ummarta masu shekaru daga,15 zuwa 64 da suka kai milyan 2 da suke rayuwa da cutar HIB.
“Kasar tana ci gaba da fuskantar matsala dangane da yadda ake kamuwa da cutar ko yadda ta ke shiga daga uwa zuwa danta tun yana cikin mahaifa. Rahoton UNAIDS na 2023 ya nuna kusan yara 160,000 da shekarunsu daga 0-14 ke rayuwa da cutar HIB, yayin da aka samu mutane 22,000 da suka kamu da cutar sai kuma mutum 15,000 da suke mutuwa duk shekara,a sanadiyar cutar kamar yadda ta yi bayani.
Sai dai kuma duk da hakan tace ma’aikatar lafiya ta tarayya da walwalar jama’a, kamar yadda Dokta Ilori ta bayyana bada dadewa bane ta kafa wani kwamitin kasa wanda zai domin ya tabbatar da ana aiwatar da abinda aka yi niyyar yi.
Ta kara jaddada NACA ta kaddamar da kwamiti a Jihohi uku inda ta fara magana kai tsaye da gwamnoni uku su bada taimako kaddamarwar da za’ayi, da kuma samar da wani kwamiti kamar shi a zaman na bangaren Jiha,da niyyar tabbatar da ba wani jaririn da za’a sake haifa dauke da cutar HIB a Nijeriya.
“Wannan abin haka zai kasance a Jihohi 36 da babban birnin tarayya bada dadewa ba ,” ta kara jaddada shirin hukumar dake yi ma jagoranci da zata ci gaba duk wasu tsare- tsaren taimakawa kawo karshen cutar kanjamo, koda kuwa ace su masu taimakawar za su nuna gazawa ko su bari.
“Tawaga ta, ta dade tana ganawa da masu ruwa da tsaki kan lamarin HIB wajen taimakawar da suke yi, inda har ma suna samar da wani hali na yiyuwar ci gaba dayin hakan domin kada a bari a tafka asarar nasarar da aka fara samu.Daga nan kum a samu damar sa gwamnatcin Jihohi a cikin lamarin inda ita ma za ta bada nata taimakon wajen samar da duk abubuwan da ake bukata lokacin aiwatar da tsarin a Jihohi.
“Manufar wannan dabarar kamar yadda ta yi karin bayani koda ace su masu taimakawa sun daina, babu wani abinda zai tada hankalin kasa, idan dai ana maganar matakan hana yaduwa da kawo karshen cutar HIB, har ma da wasu cututtukan da suke da alaka da ita.