ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yanke Wa Mutane 2,512 Hukunci Kan Ta’addanci, An Ɗauki Matakin Hukunta Masu Taimaka Wa ’Yan Ta’adda A Nijeriya

by Sadiq
43 minutes ago
Ta'addanci

Gwamnatin Nijeriya ta samu nasarar yanke wa mutane 2,512 hukunci a shari’o’in da suka shafi ta’addanci a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC).

Mai kula da cibiyar, Manjo Janar Adamu Laka ne, ya bayyana hakan a Abuja ranar Talata yayin gabatar da sakamakon shari’o’in ta’addanci karo na 11.

Ya ce an saurari ƙararraki 1,069 tsakanin 15 zuwa 24 ga watan Oktoba.

ADVERTISEMENT

Daga cikin waɗanda aka gurfanar, an yanke wa mutum 791 hukunci, yayin da aka wanke mutum bakwai.

Laka ya ce gwamnati ta mayar da hankali wajen hukunta mutanen da ƙungiyoyin da ke taimaka wa ’yan ta’adda ta hanyar ba su kuɗaɗe, kayan aiki da sauran tallafi.

LABARAI MASU NASABA

Trump Ya Ɗora Alhakin Shan Kayen Da Jam’iyyarsa Ta Yi Kan Yaƙin Iran Yayin Da Democrat Ta Yi Nasara

Bashin Da Ake Ci Na Barazana Ga Tattalin Arziƙin Nijeriya – Sanusi II

Ya bayyana cewa an kuma saurari kararraki 201 da suka shafi samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan ta’addanci a wannan karo.

A nasa ɓangaren, Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA) ya yi gargadin cewa duk wanda ya san yana taimaka wa ’yan ta’adda zai iya fuskantar hukunci, ko da kuwa ba da shi aka kai hare-haren ba.

Daraktan Sashen Shari’a na ONSA, Zakari Mijinyawa, ya ce dokar ƙasar ta tanadi zaman gidan yari na aƙalla shekaru 20 ga duk wanda ya taimaka wa ayyukan ta’addanci.

Ya buƙaci ’yan Nijeriya su fahimci tanade-tanaden dokar, yayin da jami’an gwamnati suka tabbatar da cewa za a bai wa duk wadanda ake tuhuma damar samun shari’a ta gaskiya da kuma wakilcin lauya.

MASU ALAKA

Trump Ya Yi Barazanar Ƙaƙaba Haraji Kan Ƙasashen Da Ke Kasuwanci Da Iran
Kasashen Ketare

Trump Ya Ɗora Alhakin Shan Kayen Da Jam’iyyarsa Ta Yi Kan Yaƙin Iran Yayin Da Democrat Ta Yi Nasara

November 4, 2026
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba
Manyan Labarai

Bashin Da Ake Ci Na Barazana Ga Tattalin Arziƙin Nijeriya – Sanusi II

November 4, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Manyan Labarai

Za Mu Biya Ma’aikata Alawus ɗin Sufuri na Naira 70,000 — Gwamnatin Kebbi

November 3, 2026

LABARAI MASU NASABA

An Yanke Wa Mutane 2,512 Hukunci Kan Ta’addanci, An Ɗauki Matakin Hukunta Masu Taimaka Wa ’Yan Ta’adda A Nijeriya

An Yanke Wa Mutane 2,512 Hukunci Kan Ta’addanci, An Ɗauki Matakin Hukunta Masu Taimaka Wa ’Yan Ta’adda A Nijeriya

November 4, 2026
Sarkin Daura Ya Nemi Ake Yanke Wa Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi Hukuncin Kisa

Sarkin Daura Ya Nemi Ake Yanke Wa Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi Hukuncin Kisa

November 4, 2026
Farashin Man Fetur Ya Haura N1,370 Kan Kowace Lita A Legas

Farashin Man Fetur Ya Haura N1,370 Kan Kowace Lita A Legas

November 4, 2026
Trump Ya Yi Barazanar Ƙaƙaba Haraji Kan Ƙasashen Da Ke Kasuwanci Da Iran

Trump Ya Ɗora Alhakin Shan Kayen Da Jam’iyyarsa Ta Yi Kan Yaƙin Iran Yayin Da Democrat Ta Yi Nasara

November 4, 2026
ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

November 4, 2026
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Bashin Da Ake Ci Na Barazana Ga Tattalin Arziƙin Nijeriya – Sanusi II

November 4, 2026
Badakalar Rajistar Masu Zaɓe: Ezekwesili Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Mai Zaman Kansa

Badakalar Rajistar Masu Zaɓe: Ezekwesili Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Mai Zaman Kansa

November 4, 2026
Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

November 3, 2026
Hanyar Abuja-Kaduna: Ci Gaban Aikin Gyara Ya Farfaɗo Da Fatan Matafiya

Hanyar Abuja-Kaduna: Ci Gaban Aikin Gyara Ya Farfaɗo Da Fatan Matafiya

November 3, 2026
An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

November 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.