Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane a wani samame da suka kai dajin Edimogbo, da ke Ƙaramar Hukumar Igalamela/Odolu a Jihar Kogi.
Samamen ya gudana ne ranar 3 ga watan Nuwamba, bayan wani farmaki da sojojin suka kai maboyar waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar 2 ga watan Nuwamba.
Sojojin sun ce sun ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu, jakar alburusai guda bakwai, dubban alburusai, wayoyin hannu guda biyu da kuma na’urar cajin waya.
Rundunar Sojin ta ce aikin na daga cikin ƙoƙarinta na yaƙi da masu garkuwa da mutane, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma dawo da zaman lafiya a Jihar Kogi.














