ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Bindiga Sun Sace Amarya Da Baƙin Biki A Sokoto

by Abubakar Sulaiman
11 months ago
Bindiga

Ƴan bindiga sun kai farmaki a daren Asabar a garin Chacho na ƙaramar hukumar Wurno a Jihar Sokoto, inda suka sace amarya, da ƙawayenta da wasu baƙin biki da suka taru domin shirye-shiryen bikin aurenta da aka tsara za a yi washegari. Shaidu sun ce maharan sun shigo ne da tsakar dare suna harbe-harbe kafin su tafi da matan da suka taru wajen sha’anin wa amaryar.

Rahotanni sun nuna cewa an kasa samun jami’an ƴansanda domin tabbatar da batun, sai dai shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon. Isah Sadeeq Achida, ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da mazauna garin, koda yake bai tabbatar ko amaryar na cikin waɗanda aka tafi da su ba. Wannan lamari ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan an biya harajin fansa na naira miliyan huɗu da babur ga wasu masu garkuwa a Rabah.

  • Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
  • Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Wani mazaunin yankin, Salisu Wurno, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa mata, da yara da tsofaffi sun tarwatse cikin dazuka domin tsira da rayukansu. Ya ce har zuwa yanzu maharan ba su tuntuɓi iyalin amaryar ko shugabannin al’ummar yankin ba, lamarin da ya ƙara tayar da hankulan jama’a game da halin da waɗanda aka sace ke ciki.

ADVERTISEMENT

Har yanzu hukumomi ba su fitar da sanarwa ba, yayin da mazauna Chacho ke roƙon gaggawar ɗaukar matakin jami’an tsaro domin daƙile yawaitar hare-haren da suka addabi yankin.

Al’ummar garin sun ce tsaro ya ƙara taɓarɓarewa a maƙwabtan yankuna, abin da ya jefa su cikin tsananin fargaba.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

Bindiga
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna
Manyan Labarai

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume
Manyan Labarai

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Sake Garkuwa Da Wani Manomi A Kwara

Ƴan Bindiga Sun Sake Garkuwa Da Wani Manomi A Kwara

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.