Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman, na don bibiyar shirin zaɓen Nijeriya, wanda zai ba hukumar damar sa ido kan shirye-shiryen zaɓe a duk jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja nan take, yayin da rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta kai miliyan 100 gabanin zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan shi ya bayyana haka a ranar Litinin, yayin da yake buɗe taron bita na tsare-tsaren aiki na tsawon kwanaki biyu ga sakataran gudanarwa, wanda aka yi a otal ɗin Marriott da ke Ikeja a Jihar Legas.
Farfesa Amupitan ya ce bitar aikin za ta samar da samfurin bin diddigin aikin mataimakin sakataren gudanarwa na ‘Excel’ da aka daidaita, wanda ke haɗe kai tsaye da allon aikin cibiyar kula da zaɓe na hukumar da kuma tsarin aikin zaɓe.
Ya ƙara cewa hukumar a tarihi ba ta da wata hanya ta musamman da take bin diddigin ayyukan gudanarwa na sakataran gudanarwa, yana bayyana sabon kayan aikin a matsayin wanda zai cike wannan giɓin na hukuma.A cewarsa, idan an tura shi, mai bibiyar zai ba shugabannin zaɓe na jihohi da kwamishinonin masu sa ido da sakataren kwamitin da hedkwata damar ganin rabon kayan aiki, horon wucin-gadi ga ma’aikata da shirin jihohi nan take, yana maye gurbin tsoro saboda rashin sani da sarrafa abubuwa kafin lokaci.
Shugaban INEC ya ce wannan sabuwar hanyar za a yi amfani da ita a zaɓen 2027, tana zama wani tsari na dindindin na koyar da sabbin ma’aikatan gudanarwa a nan gaba.
Ya haɗa wannan shiri da ƙoƙarin hukumar na tabbatar da tsabtace rajistar masu kaɗa ƙuri’a da kuma tattara katin zaɓe yayin da rajista ke kusantar miliyan 100, yana bayyana rajistar masu kaɗa ƙuri’a a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan aiki biyar da ake duba a taron bitar tare da kula da kayan aiki da sarrafa su, fasahar zaɓe, inganta ma’aikata na wucin-gadi, da bin ƙa’idojin kuɗi.
Amupitan ya ce shirin bibiyar zaɓe yana ginuwa ne kan darussan da aka koya daga zaɓukan baya a ƴan kwanakin nan, ciki har da zaɓen gwamnan Jihar Osun, inda kyakkyawan tsari na kayan aiki da fasaha suka samar da sakamako mai kyau.Ya ce hukumar tana aiki yanzu don sanya wannan ƙa’idar ta zama ta ƙasa baki ɗaya a cikin watanni shida da suka rage kafin zaɓen 2027.
A cikin jawabinsa, kwamishinan zaɓe na Jihar Legas ya bayyana taron a matsayin wanda ya zo a kan lokacin da ya kamata a yi shirye-shiryen hukumar, sannan ya yaba wa Tarayyar Turai, ta hanyar tallafin Tarayyar Turai ga mulkin dimokiradiyya a Nijeriya (EU-SDGN), wanda ‘Development Alternatives Incorporated’ (DAI) ke aiwatarwa, kan goyon bayan wannan aiki.
Haka kuma sakataren hukumar, Mrs Rose Oriaran-Anthony, ta ce taron zai tabbatar da cewa shalkwatan hukumar da dukkan jihohi suna aiki ne bisa tsarin ayyukan zaɓe guda, tare da bai wa sakataren gudanarwa ilimi na zamani game da sabbin manufofi, fasaha da hanyoyin gudanarwa kafin zaɓen shekarar 2027.
Ta ce ana sa ran kowace wakilcin jiha zai bar taron bita da rajistar haɗarin kayan aiki, tsari na ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi, da shirin haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki na watanni uku masu zuwa, tare da sabon samfuri na bibiyar aiki.
Taron bita da aka shirya ƙarƙashin jagorancin ofishin sakataren hukumar tare da tallafi daga DAI-EUSDGN, ya samu halartar kwamishinonin zaɓe dukkan jihohi da daraktan janar na cibiyar zaɓe da daraktoci daga shalkwatan hukumar da sakatarorin gudanarwa daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.














