Yau Juma’a, ma’aikatun kasar Sin guda tara, cik har da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa, sun wallafa wani shiri mai suna “Shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa masana’antar kera motoci masu aiki da sabbin makamashi da fasahohin basira da sadarwa”, wanda ya yi nuni da cewa, nan da shekarar 2030, za a kara karfafa fifikon da kasar Sin ke da shi a dukkan jerin sana’ar, sannan za ta shiga sahun manyan kasashe masu kera motoci a duniya.
A kasuwar cikin gida kuma, motocin fasinja masu aiki da sabbin makamashi za su kai kashi 70% na jimillar sabbin motocin da ake sayarwa a bangarensu, yayin da motocin kasuwanci masu aiki da sabbin makamashi za su kai kashi 40% na jimillar sabbin motocin da ake sayarwa a nasu bangare. Bugu da kari, za a kara amfani da motocin dake iya tuka da kansu ba tare da direba ba, har ma su zama gama gari.
Motoci masu aiki da sabbin makamashi da fasahohin basira da sadarwa su ne babban alkibla na ayyukan sauyi da habakar masana’antar kera motoci.
Shirin ya bukaci a karfafa da fadada fifikon da kasar Sin ke da shi a wannan fanni, domin ya zama ginshiki mai karfi ga cimma zamanantarwa irin ta kasar Sin da kuma gina kasar Sin da za ta zama kasa mai karfi dake bin tsarin gurguzu. ( Bilkisu Xin)













