A halin yanzu ana gudanar da bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa ta Sin CIFTIS na shekara ta 2026 a birnin Beijing. Wannan bikin ya jawo kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 90, kuma kamfanoni sama da 1,800 sun shiga cikin baje kolin, ciki har da kamfanonin Afirka da yawa da suka shiga ta hanyar yanar gizo ko kuma a zahiri.
Akwai wani canji da ke faruwa da ya kamata a kula da shi, hadin gwiwar hada-hadar ba da hidima tsakanin Sin da Afirka tana tafiya daga “fitar da fasaha kawai” zuwa “karfafa karfinsu cikin hadin gwiwa da cin moriya tare”.
Shirin bunkasa hada-hadar ba da hidima na ma’aikatar kasuwanci ta Sin da sauran hukumomin da abin ya shafa ya nuna cewa, “dagewa kan daidaita cinikin shige da fice, da inganta daidaiton ci gaban hada-hadar ba da hidima” shi ne alkiblar da aka tsayar don ci gaban hadar-hadar ta Sin. Ana iya aiwatar da hada-hadar ba da hidima ta hanyar yanar gizo da kashe kudade a ketare, ko kuma ta hanyar zuba jari a fannin hada-hadar ba da hidima a kasashen waje.
A cikin ‘yan shekarun nan, hada-hadar ba da hidima tsakanin Sin da Afirka tana samun kwaskwarima daga fitar da fasaha kawai zuwa “mika fasaha + karfafa karfin hadin gwiwa da cin moriya tare + more kasuwanni tare”, matakin da ya dace sosai da tsare-tsaren da ke cikin takardun sakamakon dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na “karfafa mika fasahohi da raba ilimi” da kuma “tallafa wa Afirka inganta karfin kirkire-kirkire”.
A watan Agusta na shekara ta 2026, reshen bankin Standard Bank a Kenya ya fara aiki da tsarin biyan kudi na kasa da kasa na kudin Sin Yuan CIPS, inda ya kammala ciniki na farko na Yuan a kasuwar Kenya. Wannan ba wai kawai ya rage hadarin canjin kudi a cinikayyar Sin da Afirka ba, har ma ya tallafawa kamfanonin Afirka don shiga kasuwar Sin a bangaren hada-hadar kudi, hada-hadar ba da hidima a harkar kudi ba wai “Sin ta bayar, Afirka ta yi amfani da ita” kawai ba, a hakika dai ya kasance matakin hadin gwiwar bangarorin biyu da samun moriya tare.
Kamfanonin Sin suna karbar kwangilar ayyukan gine-gine da yawa a Afirka. A shekara ta 2025, yawan kudin dake shafar kwangilar gine-gine da Sin ta kammala a Afirka ya kai kusan dala biliyan 45.
Daga layin dogo zuwa tashar jiragen ruwa, daga tashar wutar lantarki zuwa gada, Sin ta taka rawar gani wajen gina manyan ababen more rayuwa a Afirka, ba wai kawai suna fitar da fasaha ba, har ma tana daukar ma’aikatan Afirka da horar da su a fannin fasaha, ta kuma horar da dubban injiniyoyi da ma’aikatan fasaha na Afirka.
Kamfanin jirgin saman Habasha daya ne daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama a Afirka, yana tafiyar da hanyoyin jiragen sama da yawa kai tsaye tsakanin Sin da Afirka. A watan Agusta na shekarar bana, kamfanin ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da kamfanin AVIC International na Sin, don sayen jirgi mai samfurin C919 kerar Sin, inda ya zama kamfanin jiragen sama na farko na Afirka da ya sayi babban jirgin sama da Sin ta kera. Afirka sabon wuri ne na yawon shakatawa ga Sinawa, kuma kasashe kamar Masar da Afirka ta Kudu da Kenya da Morocco suna karbar ‘yan yawon shakatawa na Sin da yawa a kowace shekara. Zurfafa hada-hadar ba da hidima a bangaren jiragen sama yana samarwa Sinawa saukin bude ido a Afirka a ko da
Tsarin hasashen ibtila’in sauyin yanayi na “Mazu” misali ne na musamman na “hadin gwiwar Sin da Afrika wajen zurfafa karfinsu” a hada-hadar ba da hidima. Wannan tsarin ya fara aiki a kasashe 7 ciki har da Jibouti da Habasha, kuma yanzu ya riga ya ba da hidima ta yanar gizo ga kasashe sama da 40. A watan Yulin bana, an mika sabon nau’in tsari da aka sabunta wato Mazu 2.0 cikin nasara. Abin da Sin ke bayarwa ba manhaja da ba a iya sarrafawa ba, a maimakon haka ta bayar da cikakken shirin dake dacewa da yanayin wuri don horar da fasaha da samar da tallafi a dogon lokaci.
Babban jigon irin wannan hada-hadar ba da hidima ba “sayar da kayayyaki” kawai ba ne, Sin tana fatan karfafa karfin Sin da Afrika cikin hadin gwiwa don samun ci gaba tare, saboda guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni.
Bikin hada-hadar ba da hidima ba wai kawai jagorar hada-hadar ba da hidima ta duniya ba ne, har ma shaida ce ta hadin gwiwar Sin da Afirka daga “hadin gwiwa a kan ababen more rayuwa kawai” zuwa “hadin gwiwa don karfafa karfi tare da samun moriya tare”.
Lokacin da aka kammala ciniki na farko bisa kudin Sin Yuan a Kenya, da hanyoyin jiragen sama tsakanin Sin da Afirka ke ci gaba da bunkasa yawon shakatawa na bangarorin biyu, da tsarin hasashen ibila’in sauyin yanayi na “Mazu”, wadannan al’amura dake faruwa a sassan daban-daban a Afirka, suna haduwa zuwa sabon karfi na hadin gwiwar Sin da Afirka musamman hada-hadar ba da hidima, wato ba “fitar da fasaha kawai” Sin take yi ba, karfafa karfinsu cikin hadin gwiwa da samun moriya tare ake kokarin aiwatarwa.(Marubuciya: MINA)














