ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

by Sulaiman and Leadership Hausa
46 minutes ago

Mrs Zubaida Umar, Darakta-Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta yi fice ta hanyar shugabanci mai ma’ana da mai saurin mayar da martani, tana jagorantar wani babban sauyi a yadda Nijeriya ke gudanar da harkokin agajin gaggawa. Tun bayan da ta karɓi ragamar jagorancin hukumar, ta himmatu wajen canza tsari daga yadda ake mayar da martani ga agajin gaggawa ne kawai zuwa wani sabon tsarin da ke mai da hankali kan rage haɗarin bala’o’i, shiri, gargaɗi na gaggawa da ɗaukar matakin rigakafi.

Jagorancinta ta ƙarfafa damar NEMA wajen gano sabbin haɗari, tara masu ruwa da tsaki da tsara hanyoyin da za a ɗauka mataki tare da mayar da hankali ga al’ummomin da suke cikin haɗarin ambaliyar ruwa, rikici da sauran masu mutanen da ke buƙatar samun agajin gaggawa.

A wannan tsari akwai haya ingantacce wajen gudanar da agajin gaggawa ba wai kawai ɗaukar mataki bayan an samu hatsari ba, har ma don hana ko rage illolinsa ta hanyar samun bayanai a kan lokaci, shiri da aiki tare da juna.Babban abin da ya bambanta shugabancinta shi ne, ƙarfafa tsarin sanarwa da shirin gaggawa na Nijeriya. Ganin yadda agajin gaggawa ke ƙaruwa da tsanani, Mrs Umar ta mayar da hankali wajen haɗa kai da manyan cibiyoyin fasaha da ayyuka, ciki har da hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) da hukumar kula da ruwa ta Nijeriya (NIHSA) da hukumar sadarwa ta Nijeriya (NCC) da hukumar bincike da ci gaban sararin samaniya ta ƙasa (NASRDA) da rundunar sojojin Nijeriya da hukumar kula da agajin gaggawa ta jihohi da kuma abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.A ƙarƙashin jagorancinta, NEMA ta taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kai don bunƙasa shirin faɗakarwa tun da wuri ga kowa (EW4All) a Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Shirin yana haɗa muhimman hukumomi don ƙarfafa sani game da haɗari, hasashen abubuwa, yaɗa faɗakarwa, sadarwa da shirin ɗaukar mataki da wuri. Wannan hanyar na taimakawa wajen tabbatar da bayanan faɗakarwa tun da wuri ana maida su zuwa matakan da ke kare rayuka, hanyoyin rayuwa da al’ummomi.

Mrs Umar ta kuma ƙarfafa shirin ɗaukar matakin rigakafin ambaliyar ruwa ta hanyar ci gaba da tuntuɓar jihohi da hukumomin da abun ya shafa. Bisa ga hasashen yanayi na kakar da kuma bayanan ambaliyar shekara-shekara, NEMA ta ƙara yawan faɗakarwa a faɗin ƙasa, tuntuɓar masu ruwa da tsaki, gudanar da shiri na musamman da kuma tura kayan aikin agajin gaggawa a wuraren da aka gano suna cikin haɗari. Ta riƙa ƙarfafa al’umma a wuraren da ke cikin haɗari su saurari gargaɗin hukuma, su koma inda ya dace, kuma su ɗauki matakan kariya kafin hatsari ya faru.Wani muhimmin abu a shugabancinta shi ne, amfani da fasaha da kimiyya a cikin gudanar da harkoki agaji. NEMA ta ƙarfafa haɗin kai da NASRDA da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Harkokin Sararin Samaniya don amfani da fasahohin sararin samaniya, hangen nesa da kayan aikin na zamani da ke tasowa don sa ido kan haɗarin da shirye-shiryen gaggawa. Hukumar ta kuma tallafa wa shirye-shirye don inganta samun bayanai da sadarwa yayin agajin gaggawa, ciki har da amfani da hanyoyin tauraron Ɗan’adan don inganta haɗin kai wajen aiki.Don ƙarfafa gudanar da agajin gaggawa bisa hujja, Mrs Umar ta yi haɗin gwiwa da cibiyar ayyukan agajin gaggawa ta ƙasa don daidaita, sarrafa da nazarin sahihan bayanai kan ambaliyar ruwa da sauran bala’o’in yanayi.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

Wannan ya ƙara wayar da kai kan yanayi, sarrafa bayanai da yanke shawara, kuma ya samar da dandamali mai ƙarfi don daidaita ayyukan agajin gaggawa.A lokacin da ta kasance a muƙamin, ta mayar da hankali kan gina ƙarfin ƙwararrun ma’aikatan agajin gaggawa. Ma’aikatan NEMA da sauran masu ruwa da tsaki sun halarci horo ta musamman.Haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, cibiyoyin ilimi da ƙungiyoyin duniya ya ƙara faɗaɗa damar musayar ilimi, bunƙasa ƙwarewa da inganta shiri na aiki.

Bayan shirin tsaro da gyaran hukumomi, Mrs Umar ta nuna jagoranci mai tausayi a fannin taimakon jama’a. A ƙarƙashin jagorancinta, NEMA ta tsara yadda za a bai wa dubban gidaje ga mutanen da bala’o’i suka shafa kamar ambaliyar ruwa, guguwar iska, gobara, rikice-rikice da sauran agajin gaggawa taimako.

Ta kasance a kullum tana jaddada cewa duk irin taimakon jama’a dole ne a kai shi lokaci-lokaci, a buɗe, a bayyane kuma ya dace da haƙiƙanin buƙatun mutanen da lamarin ya shafa.Shagabancinta ya kuma ƙarfafa haɗin gwiwar jin kai na ƙasa da ƙasa, ta gano cewa yanayin hatsarin da Nijeriya ke fuskanta na ƙaruwa da rikitarwa yana buƙatar ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin ƙasar da ƙungiyoyin jin kai da sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

Mrs Umar ta ƙara nuna jagoranci mai kyau a shirin sake farfaɗowar mutane da rikici ya shafa (RSPIC), wani shiri da aka ƙirƙira domin tallafa wa al’ummomin da rikici ya shafa. Ta hanyar rawar da NEMA ke takawa wajen tsara wannan shiri, shirin ya nuna fahimta mai zurfi game da sarrafa haɗura wanda ya wuce tallafin gaggawa kawai har zuwa farfaɗowa, dawo da martaba, da sake gina hanyoyin rayuwa.

Jagorancinta ta ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin soja da farar hula da kuma tsakanin hukumomi. Hulɗa da sojan Nijeriya, rundunar sojin sama ta Nijeriya da sauran hukumomin tsaro sun mayar da hankali kan amfani da ƙwararrun ma’aikata, fasahar na’ura, kayan aiki da rukunin martani na bala’i don inganta aikin ceto da ayyukan agajin gaggawa. Wannan fasaha ta haɗin gwiwa tana gano cewa ingantaccen gudanar da agaji yana buƙatar haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, abokan agaji, al’ummomi da kuma sashen masu zaman kansu.Wata muhimmin tsari na shugabancin Mrs Umar shi ne, himmarta wajen gyaran cibiyoyi da kawo tsare-tsare.

Haɓaka tsarin dabarun NEMA, bitar manyan tsare-tsare na ƙasa kan kula da bala’o’i, da ƙoƙarin ƙarfafa tsarin kula da agagin gaggawa na jihohi da ƙananan hukumomi wajen gina tsarin da zai ɗore maimakon dogaro kawai da matakan gaggawa.Ta hanyar waɗannan ayyuka, Hajiya Zubaida Umar ta kawo hanyar jagoranci a aikin gwamnati wadda ke bayyana a zahiri da haɗin kai da tausayi da bibiyar harkokin kuɗaɗe. Ta ci gaba da mayar da NEMA zuwa wata hukuma mai saurin ɗaukar mataki, mai amfani da fasaha da kuma mayar da hankali ga mutane, wanda ya fi dacewa wajen tunkarar yanayin haɗarin mai rikitarwa a Nijeriya.

A saboda jagorancinta mai ma’ana da ƙwazonta wajen tallafa wa ‘yan Nijeriya masu rauni, Hajiya Zubaida Umar ta cancanci lambar yabo ta zama gwarzuwar ma’aikaciyar gwamnati ta wannan shekarar ta Jaridar LEADERSHIP.

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?
  • Sulaiman
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • Sulaiman
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari
  • Sulaiman
    Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
Leadership Hausa
Website |  + posts Bio
  • Leadership Hausa
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari
  • Leadership Hausa
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Leadership Hausa
    Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari
Labarai

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Next Post
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.