Yayin da taron koli na kungiyar BRICS na 18 ke tafe a bana, wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin mutane masu bayar da amsa 12,250 a fadin kasashe 41 ya nuna cewa, sama da 6 cikin 10 na mutanen sun yi imanin cewa, kungiyar BRICS ta kara zama mai tasiri cikin harkokin kasa da kasa a shekarun baya bayan nan. Masu bayar da amsar na ganin kungiyar tana taka rawa a matsayin karfi da ke jagorantar kasashe masu tasowa wajen inganta shugabancin duniya da tabbatar da oda da daidaito da adalci a duniya.
Cikin nazarin, kaso 63 na masu bayar da amsa sun bayyana gamsuwa da gudunmuwar da BRICS ke bayarwa ga inganta tsarin shugabancin duniya. Gamsuwar da masu bayar da amsa daga kasashe 25 cikin kasashen 41 suka nuna, ya kai fiye da kaso 60.
Bangarori 3 da aka fi amincewa da su su ne: BRICS ta taimaka wa kasashe masu tasowa wajen inganta farfado da tattalin arzikin duniya da bunkasa cinikayya. Na biyu, BRICS ta inganta yi wa tsarin shugabancin duniya garambawul da karfafa jin muryoyin kasashe masu tasowa. Bangare na uku shi ne, ta tallafa wa hadin gwiwar kasa da kasa a harkokin cinikayya tare da adawa da kariyar ciniki da takumkumai daga bangare guda. (Fa’iza Mustapha)














