Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Juma’a 11 ga wannan wata cewa, kasar Sin ba ta killace kirkire-kirkirenta, tana son cin moriya tare da sassan duniya a fannin kirkire-kirkire.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a kwanakin baya hukumar bayar da shaidar ikon mallakar kirkira ta duniya ta gabatar da rahoton tantance yankunan yin kirkire-kirkire mafiya karfi guda 100 da ke kan gaba a duniya, inda kasar Sin take da yankuna 25 da suka shiga jerin sunayen, kana yawansu ya kasance a matsayi na farko cikin shekaru 4 a jere.
Game da wannan batu, kakakin ta bayyana cewa, yin kirkire-kirkire shi ne muhimmin abin da ke sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da inganta sana’o’i a kasar Sin.
Yin kirkire-kirkire da samun ci gaba a kasar Sin, ya samar da dama ga duniya, inda karin kamfanonin kasashen waje suka zabi yin nazari da kirkire-kirkire a kasar Sin, don inganta karfinsu na yin takara a duniya a babbar kasuwar kasar Sin. (Zainab Zhang)














