Buba Galadima, jigo a jam’iyyar NDC, ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam’iyyar APC da hana ’yan adawa gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin ’yanci gabanin zaɓen 2027.
Da yake magana a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise, Galadima ya yi zargin cewa ana kai wa wasu ’yan adawa hari ko kuma hana su yin kamfen a wasu sassan ƙasar.
Ya ce irin wannan takura ta saɓa wa tsarin dimokuraɗiyya, wanda ya kamata ya bai wa mutane ’yancin faɗin albarkacin baki, zirga-zirga da shiga harkokin siyasa.
Galadima ya kuma nuna damuwa kan yadda ake aiwatar da dokar kashe kuɗin kamfen.
Ya ce tsadar allunan tallan siyasa na iya sa jam’iyyu kasa bin dokar Naira biliyan 10 da dokar zaɓe ta ƙayyade.
Ya yi iƙirarin cewa a wasu jihohi, allon talla guda ɗaya na iya kai wa Naira biliyan ɗaya, lamarin da zai iya sa kuɗin kamfen a faɗin ƙasar ya wuce iyakar da doka ta tanada.














