Yayin da ake tunkarar babban zaben 2027, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa cewa amfani da kalaman cin mutunci, rashin da’a ko kuma kalaman tunzura jama’a a lokacin yakin neman zabe na iya jawo musu tarar makudan kudade da kuma yiwuwar daurin gidan yari, bisa tanadin Dokar Zabe ta 2026.
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sabbin barazanar da wasu masu rike da mukaman siyasa ke yi wa masu kada kuri’a da ke nuna adawa da ra’ayoyinsu.
Babban Sakataren Yada Labarai/Mai ba Shugaban INEC shawara kan harkokin yada labarai, Mista Adedayo Oketola, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin Vanguard a ranar Lahadi.
Oketola ya ce kalaman yakin neman zabe suna ketare iyakar abin da doka ta amince da shi zuwa matakin tsoratar da masu kada kuri’a ne idan suka wuce muhawarar siyasa ko suka mayar da hankali kan sukar manufofi, koma tilastawa, kalaman kiyayya ko barazanar cutar da wasu.
Ya ce, “A karkashin tsarin dokokin Nijeriya, kalamai suna zama abin hukunta mutum a matsayin tsoratarwa ne idan suka tunzura kiyayyar kabila, addini ko yankin kasa ta hanyar amfani da kalaman cin mutunci, wulakanci ko bata suna da aka tsara kai tsaye domin tayar da hankulan jama’a ko kai hari ga wasu kungiyoyi.”
Oketola ya ce wannan tanadi yana karkashin Sashe na 96 na Dokar Zabe ta 2026.














