Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya buƙaci Sanata Abdul’aziz Yari da ya sake yin nazari kan shawarar da ya yanke na karɓar muƙamin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Kasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce yadda aka tsara kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya nuna wa ’yan Nijeriya cewa zaɓen 2027 zai kasance fafatawa tsakanin masu son ci gaba da tafiyar da gwamnatin yanzu da kuma waɗanda ke neman sauya gwamnati.
Ya bayyana damuwa kan yadda farashin kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki ke ci gaba da tashi, rashin aikin yi, raguwar damarmaki ga matasan Nijeriya, rashin tsaro da kuma matsalolin da manoma da ’yan kasuwa ke fuskanta.
Ya kuma koka kan matsin lambar da ake fuskanta a ɓangaren ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyukan gwamnati.Don haka, Kwankwaso ya ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi amfani da babban zaɓen 2027 wajen yin watsi da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da danniya, tare da neman shugabanci mai rikon amana da kuma mai sanya muradun jama’a a gaba.
Ya ce, “Idan mutanen Osun sun iya yin hakan, to sauran sassan kasar ma za su iya.”
Kwankwaso ya yi kira na musamman ga Yari, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma fitaccen dan siyasa a yankin Arewa maso Yamma, da ya sake yin tunani kan matakin da ya ɗauka na jagorantar yaƙin neman zaɓen APC.
Ya ce, “Musamman ina kira ga dan’uwana, Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ya amince da zama Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Kasa na APC, da ya yi zurfin tunani tare da sake duba shawarar da ya yanke na karɓar wannan nauyi.”














