ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Garkuwa Da Masallata A Neja: Har Yanzu Ba Mu San Adadin Waɗanda Aka Sace Ba – Gwamnatin Jihar

by Sulaiman
2 weeks ago
Neja

Kwana huɗu bayan sace ɗimbin masu ibada a wani babban masallaci da ke yankin Dakera, a Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, gwamnatin jihar ta ce har yanzu ba ta tabbatar da ainihin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da masu ibada daga al’ummomin Gidan-Zana da Kpenya da ke Dekara, ciki har da dagacin kauyen da babban limamin masallacin, yayin gudanar da sallar Juma’a a ranar Juma’ar da ta gabata.

An ruwaito cewa kimanin masu ibada 200 ne suke cikin masallacin lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmakin bayan an kammala sallar, inda suka tilasta musu bin su zuwa cikin daji.Da yake mayar da martani kan lamarin a jiya Lahadi, gwamnatin jihar ta ce har yanzu tana kan tantance adadin mutanen da aka sace da sauran bayanan da suka shafi lamarin.

ADVERTISEMENT

Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na jihar, Obed Nuhu Nana, ya ce, “Gwamnati na kira ga jama’a, musamman mazauna al’ummomin da lamarin ya shafa, da su guji yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, adadin waɗanda abin ya shafa ko kuma bayanan da aka yi hasashe a kansu, wadanda ka iya kara jefa jama’a cikin fargaba ko kuma kawo cikas ga kokarin jami’an tsaro da suke yi na ganin an kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa.”

Nana ya bayyana cewa an tura hadin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru domin tantance halin da ake ciki, bin sawun wadanda suka aikata laifin da kuma taimakawa wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ya kara da cewa, “Saboda yanayin sirrin aikin da ake gudanarwa a halin yanzu, ba za a bayyana cikakkun bayanai kan zirga-zirga da yadda aka jibge jami’an tsaro ba a wannan lokaci.”

Neja
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Cutar Apollo Na Yaɗuwa A Bauchi, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ya Kamu

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.