Gwamnatin Jihar Zamfara ta kaddamar da shirin horas da sabbin zaratan jami’an tsaron sa-kai da ta dauka domin dakile hare-haren ‘yan bindiga a karkashin kungiyar CPG a takaice.
Bayanai na nuni da cewa an zabo jami’an tsaron na CPG ne daga dukkanin masarautu 19 da ke fadin jihar.
Yayin da ya ke jawabi a wajen taron kaddamar da aikin horas da sabbin jami’an tsaron, gwamnan Jihar, Bello Matawalle, ya sha alwashin aiwatar da karin matakan yaki da ta’addanci a jiharsa, la’akari da mummunan halin da ‘yan bindiga suka jefa dubban mutane musamman a yankunan karkara.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Zamfara, ta sanar da yanke shawarar bai wa al’ummar jihar damar mallakar bindigogi domin kare kansu daga ta’addancin ‘yan bindiga.
Zamfara da ke kan gaba a tsakanin jihohin arewacin Nijeriya masu fama da hare-haren ‘yan bindiga, a baya mahukuntan jihar sun sha yunkurin kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan ta’addan, amma lamarin ya ci tura.