A makon da ya gabata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin, Mr. Wang Yi, ya kammala ziyararsa a wasu kasashen Afirka da suka hada da Namibia, Jamhuriyar Congo, Chadi da kuma Nijeriya.
Mr. Wang ya samu kyakkyawar marhabin a wadannan kasashe da ya ziyarta. Kuma wannan ziyara tashi tana matsayin kara jaddada manufar taron kolin nan da aka gudanar a birnin Beijing a shekarar da ta gabata tsakanin Sin da kasashen Afirka, inda aka cimma yarjejeniyar cude-ni- in-cude-ka, wato tsakanin Sin da kawayenta kasashen Afirka.
- Gwamnan Zamfara Ya Yaba Wa Rundunar Tsaro Tare Da Jajanta Wa Al’ummar Da Harin Jirgin Sojin Ya Shafa A Jihar
- Daga Cikon Benci Zuwa Cikakken Jarumin Kannywood – Abubakar Waziri
Babu shakka wannan ziyara ta Mr. Wang Yi ta kara zurfafa dangantaka tsakanin Sin da Afirka, musamman idan aka yi la’akari da cewa irin wannan ziyara ba ta da nasaba da yunkurin tsoma baki a cikin harkokin gida na kasashen Afirka, illa iyakar kokarin duba hanyoyin da Sin za ta bada gudummawarta wajen bunkasa harkokin tattalin arziki, cinikayya, al’adu, tsaro, kimiyya da fasaha, wato kamar dai yadda ministan harkokin wajen na Sin ya jaddada a ziyarar tasa, har ma ya kara da cewa Sin za ta tallafawa Nijeriya a sha’anin yaki da ta’addanci, bayar da kariya da tsaro ga zaman lafiya da kuma goyawa Nijeriya baya wajen ganin tana taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin kasa da kasa.
Matakin da Bankin Raya Kasa na Sin (CDB) ya dauka game da batun samar da zunzurutun kudi har dala miliyan 254 da digo 76 (kwatankwacin dalar Amurka miliyan 254.76) domin ci gaba da aiwatar da aikin layin dogo a Nijeriya, ya kara tabbatar da gaskiyar kalaman Mr. Wang na cewa China tana daukar batutuwan da suka shafi kasashen Afirka da muhimmanci.
Shi dai wannan layin dogo mai tsawon kilomita 203, wanda zai sada biranen Kano da Kaduna, idan aka kammala shi zai taimaka wajen bunkasa harkokin zirga-zirgar jama’a, sannan kuma zai habaka harkokin tattalin arziki a yankin ta hanyar kafa masana’antu, abin da zai samar da aikin yi ga dimbin jama’a.
Abin lura a nan shi ne, zabar kasashen Afirka da ministocin harkokin wajen na kasar Sin suka saba yi a matsayin kasashen da za su fara kaiwa ziyara a cikin farkon shekara ya kara jaddada muhimmancin da kasar Sin take baiwa kawayenta kasashen Afirka. Dama dai China da Nijeriya sun dade suna cudanya da juna, suna mutunta juna kuma suna goyon bayan juna a muhimman batutuwa na kasa da kasa. Sabo da haka wannan ziyara ta Mr. Wang Yi ta kara zurfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu. (Lawal Mamuda)