ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwa 10 Da Tinubu Ya Bayyana A Jawabinsa Na Ranar Ƴancin Kai

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Nijeriya ta kammala wani muhimmin mataki na gyaran tattalin arziƙinta, inda gwamnati za ta mayar da hankali kan samar da abin da ya kira “wadata ga kowa”. Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga ƴan Nijeriya ranar Alhamis, 1 ga Oktoba 2026, yayin bikin cikar ƙasar shekaru 66 da samun ƴancin kai.

1. Nijeriya ta tsallake wani mawuyacin lokaci:

Shugaba Tinubu ya ce ƙasar ta riga ta wuce wani lokaci mai wahala na gyaran tattalin arziƙi, inda ya kwatanta matakin da ƙasar ta kai da “tsallakawa daga Bahar Maliya”. Ya ce yanzu lokaci ne na duban zuwa gaba maimakon komawa kan manufofin baya.

ADVERTISEMENT

2. Sauyi daga gyara zuwa wadata:

Shugaban ya ce bayan shekaru uku da gwamnatinsaa ta mayar da hankali kan gyaran matsalolin tattalin arziƙi, abin da gwamnati ta sa a gaba yanzu shi ne fannin walwala mai faɗi da za ta amfani jama’a baki ɗaya. Ya ce hakan ya haɗa da samar da ayyukan yi, inganta kasuwanci da rage matsin tattalin arziƙi.

LABARAI MASU NASABA

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

3. Ya kare manufofin gyaran tattalin arziƙi:

Shugaban Tinubu ya kare matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, ciki har da cire tallafin man fetur, yana mai cewa an ɗauke su ne domin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar tattalin arziƙin ƙasa. Ya kwatanta tsohuwar hanyar magance matsalolin da amfani da sinadarin rage zafin ciwo “morphine” wajen rage raɗaɗi ba tare da magance tushen matsalar ba.

4. An samu cigaba a wasu fannoni:

Shugaba Tinubu ya ce tattalin arziƙin Nijeriya ya samu ci gaban da ya wuce kashi huɗu a cikin 2026, yayin da ya ce hauhawar farashi ta ragu daga matakin da ta kai a baya, sannan an ƙara yawan kuɗin ajiyar waje, sannan kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta samu daidaito. Ya kuma ce kuɗaɗen da aka samu daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba sun haura dala biliyan shida a 2025.

5. Gwamnatinsa ta ƙuduri niyyar rage tsadar rayuwa

Tinubu ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen rage kuɗin samarwa da jigilar kayayyaki domin rage tsadar rayuwa. Ya ambaci faɗaɗa noman rani da ban-ruwa, da samar da iri da takin zamani, da kuma ƙara zuba jari a hanyoyi, da layin dogo da tashoshin jiragen ruwa.

6. Samar da ayyukan yi ga matasa:

Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ƙara mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, da bunƙasa masana’antu da kasuwanci. Ya kuma ambaci amfani da iskar gas wajen samar da makamashi ga masana’antu, da farfaɗo da masana’antun da suka daina aiki, da inganta fasahar zamani da koyar da matasa dabarun da kasuwar aiki ke buƙata.

7. Rage talauci zai ci gaba da zama muhimmiyar manufar gwamnatinsa.

Tinubu ya amince cewa miliyoyin ƴan Nijeriya na fuskantar ƙalubalen abinci, da kuɗin makaranta, da magani da sufuri. Ya ce gwamnati na ƙarfafa shirye-shiryen tallafa wa gidaje masu ƙaramin ƙarfi, tare da sabunta kundin bayanai na ƙasa (National Social Register) domin tallafin ya isa ga waɗanda suka fi buƙata.

8. Batun ilimi, lafiya da fansho:

Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki wajen inganta kiwon lafiya na matakin farko da ilimin bai ɗaya. Ya kuma ambaci bashin ɗalibai (Nigerian Education Loan Fund) (NELFUND) da CREDICORP a matsayin wasu daga cikin shirye-shiryen da gwamnati ke amfani da su wajen faɗaɗa damar samun ilimi da tallafin kuɗi ga ƴan ƙasa.

9. Tsaro da ƙara samar da dama ga matasa:

Shugaban ya ce an samu raguwar satar ɗanyen mai, yana mai yabawa Rundunar Soji da sauran hukumomin tsaro kan rawar da suke takawa wajen kare ƙasar da albarkatunta. Ya kuma jaddada buƙatar amfani da yawan matasan Nijeriya a matsayin wata dama ta tattalin arziƙi ta hanyar samar musu da aiki, da ƙwarewa da kuma jari.

10. Kira ga haɗin kai da duban gaba:

A ƙarshen jawabinsa, Shugaban Tinubu ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai da jajircewa, yana mai cewa sadaukarwar da aka yi yayin aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi, ai yi ne da nufin kafa tubalin ci gaba mai ɗorewa. Ya ce ƙasar ta gyara alkiblarta kuma ya kamata ƴan ƙasa su ci gaba da fuskantar abin da zai zo nan gaba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
  • Abubakar Sulaiman
    Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
  • Abubakar Sulaiman
    Aikin Titin Jirgin Ƙasa Na Kaduna Zuwa Kano Ya Kai Kashi 90%

MASU ALAKA

Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35
Manyan Labarai

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe
Labarai

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi
Labarai

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Tsarin Shugabantar Hakkokin Dan Adam A Duniya

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Tsarin Shugabantar Hakkokin Dan Adam A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.